Motoci 22 Sun Kone Yayin da Sojoji Suka Dakile Harin ISWAP a Borno
- Mayakan kungiyar ta'addanci sun yi yunkurin kai mummunan hari kan ma'aikatan agaji a yankin Monguno, jihar Borno
- Sai dai sun taki rashin sa'a domin basu tarar da ma'aikaci ko guda ba hakan yasa suka kona wasu manyan motoci da suka tarar a harabar ofishin kungiyar agajin
- Dakarun Operation hadin kai sun kuma dakile yunkurinsu na tserewa da wasu motocin hilux inda suka yi musayar wuta da su
Borno - Akalla motoci 20 ne suka kone kurmus yayin da yan ta’adda suka farmaki harabar kungiyar bayar da agaji a garin Monguno da ke jihar Borno.
An tattaro cewa yan awaren kungiyar ta’addanci na ISWAP sun farmaki garin da misalin karfe 1:00 na tsakar daren Alhamis sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi.
Wasu majiyoyin leken asiri sun fada ma Zagazola Makama cewa yan ta’addan sun yi nufin kai harin ne kan ma’aikatan agajin.
Majiyoyin sun bayyana cewa bayan ganin cewa basu tarar da kowani ma’aikaci a harabar ba, sai kawai suka kona manyan motocin SUV 18 sannan suka farfasa wasu biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan bindigar sun kuma yi yunkurin tsrewa da wasu motocin hilux kirar 4X4 guda uku amma sai sojojin Operation hadin Kai suka fafata da su.
A cewarsa, sun yasar da motocin a yayin musayar wutan da suka yi da dakarun sojin kafin suka ari na kare.
Zagazola ya fahimci cewa ba’a rasa rai ba a yayin farmakin.
Tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Neja, sun halaka mutum biyu da raunata wasu
A wani labarin, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari yankin Kaffinkoro a jihar Neja inda suka fara harbi ba kakkautawa.
A cikin haka, maharan sun sheka wasu biyan Allah biyu lahira yayin da wasu fiye da 20 suka ji rauni daga harbi.
Wannan al'amari ya sanya al'ummar yankin da ke karamar hukumar Paikoro shiga rudani da neman tudun tsira.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Emmanuel Umar, ya ce suna kokarin dawo da zaman lafiya yankin.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnati da hukumomin tsaro suna zaune kan lamarin.
Asali: Legit.ng