Matashin Kano Da Yayi Wakar Batanci Kan Manzon Allah Ya Shigar Da Kara Kotun Koli

Matashin Kano Da Yayi Wakar Batanci Kan Manzon Allah Ya Shigar Da Kara Kotun Koli

  • Yahaya Sharif-Aminu yace shifa bai yarda da hukuncin kisan da aka yi masa a jihar Kano ba
  • Mawakin begen ya shigar da kara kotun kolin Najeriya inda ya bukaci ayi watsi da dokar Shari'a
  • Kotun Shari'a dake zamanta a Kano ta yankewa Sharif-Aminu hukuncin kisa a shekarar 2020

Abuja - Yahaya Sharif-Aminu, mawakin da aka yankewa hukuncin kisa a jihar Kano a 2020 kan laifin wakan batanci kan Annabi Muhammadu (SAW) ya garzaya kotun koli.

Wannan na kunshe cikin takardun kara da lauyansa, Kola Alapinni, ya shigar rahoton Sahara Reporters.

Sharif-Aminu ya bukaci kotun kolin ta yanke hukuncin cewa batanci ga Annabi ba laifi bane a dokar Najeriya.

Hakazalika a ranar Laraba, an aikewa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da Antoni Janar na jihar, Musa Abdullahi Lawan, takardun karar.

Kara karanta wannan

Dalilin Da yasa bamu Kama Shugaban EFCC Ba har yanzu : Kakakin Hukumar Yan Sanda

Sharif
Matashin Kano Da Yayi Wakar Batanci Kan Manzon Allah Ya Shigar Da Kara Kotun Koli Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar karar da Sharif-Aminu ya shigar:

"Mai shigar da kara bai amince da sakin layi na biyu a hukuncin da kotun daukaka kara dake Kano ta yanke ba a ranar 31/08/2022 shiyasa nike shigar da kara kotun kolin Najeriya."

Ya bukaci kotun kolin tayi watsi da hukuncin kotun daukaka kara kuma a bashi nasara.

Sharif-Aminu ya bukaci kotun koli ta sanar da cewa dokar Sharia ta jihar Kano ta sabawa S.34(1)(a), S.38(1), S.39(1), na kundin tsarin mulkin Najeriya saboda haka ayi watsi da ita.

Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

Tun a 2020, kotun shari'ar a Kano ta yanke wa Shariff-Aminu hukuncin kisa bayan an kama shi da laifin batanci ga manzon Allah (SAW).

Sharif ya yi hakan ne a wata wakarsa da ta yi ta yabo a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp.

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Kotun Sin Ta Yankewa Jami’in Gwamnati Hukuncin Kisa Duk da Ya Tuba

Alkali Aliyu Muhammad Kani yace wanda ake zargin zai iya daukaka kara matukar bai gamus da hukunci da aka yanke masa ba.

Malaman jihar Kano da kungiyoyin sakai na (NGO) na jihar Kano sun nuna goyon bayansubisa hukuncin kisan da aka yankewa mawakin da yayi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Wannan ya fito ne ta wata sanarwa da shugaban kungiyar hadin guiwar, Farfesa Musa Muhammad Borodo, wanda yace kama mawakin da kuma hukuncin da aka yanke masa shine ya kawo karshen wannan lamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida