Sarkin Ogun Ya Makantar Da Ni Saboda Na Yi Rawa Da Matarsa, Mai Abinci
- Wani matashi na zargin Sarkin garinsu da fasa mai ido saboda ya yi rawa da Sarauniya a wajen Bazday
- Matashin a hira da manema labarai na kira ga hukuma ta kwato masa hakkinsa daga wajen Sarkin
- Kwamandan yan sandan yankin tuni ya ce shi fa babu yadda ya iya ba zasu iya kama sarki ba
Ogun - Wani dan kasuwa Wasiu Oduwole, ya bayyana ccewa wani Sarkin gargajiya a jihar Ogun, Oba Nureni Oduwaye, ya makantar da shi saboda yayi rawa da Sarauniyarsa.
Oduwole, wanda mai sayar da abinci ne, ya yi bayanin abinda ya faru a hirar da yayi da jaridar Punch.
Ya ce yana zamansa aka gayyacewa wani Otal a Sagamu don ya girka farfesun Kifi don murnar ranar haihuwa Bazday.
Ya ce an samu akasi farfesun bai yi dadi ba kuma wadanda suka halarci taron sun yi korafi kuma ya basu hakuri.
Oduwole yace bayan hakurin da ya bada, Sarkin ya tuhumcesa da rawa da Matarsa.
An bukaceshi yaje ya baiwa Sarkin hakuri amma yaynda yake kokarin tsugunnawa don rokon shi, Sarkin ya tokare masa ido kuma kai tsaye ya makance.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
"Kawai tsokanar Matarsa nayi cewa tsohuwa kamarta tana rawa yayinda ake wakokin zamani. Sai ya zo yana ce min wanene ni? Sai nace masa nine kanin mai Otal. Sai ya fusata ya fita daga wajen taron."
"Sai mai Otal din yace inje fadarsa in bashi hakuri, ina durkusawa in bashi hakuri ya tokareni a ido. Kai tsaye kwallon idona ya fado."
Jawabin mahaifiyarsa
Mahaifiyar Oduwole, Sakirat Oduwole, ta bayyana cewa ba tare da bata lokaci ba ta garzaya asibiti da ofishin yan sanda dake Shagamu.
Tace amma kwamansan yan sanda, Aremu Ojugbele, yace babu abinda zasuiya saboda Sarki ne kuma yafi karfin hukuma.
Tace:
Yana da Mata da yara, yanzu ya makance ba ya iya aiki. Ya ce zai bashi aikin yi amma mahaifinsana ya ce ba yarda ba, gobe zai iya sallamarsa. Kawai ya bashi milyan 1 ya kula da iyalinas, daga baya ya biya kudin asibiti zuwa Amurka a masa tiyata"
"Sai Sarkin ya bada N100,000 kacal, sai lauyanmu ya fusata da Sarkin. Sai Ya bada Cheque din N400,000. Da muka isa banki akace babu ko sisi a akawunt din.
Asali: Legit.ng