Bayan Barazanar Raba Jiha: An Yi Zaman Sulhu Tsakanin Atiku Da Kauran Bauchi
- Gudun kada a samu irin matsalar da aka samu da su Wike, Atiku ya gana da Gwamnan jihar Bauchi
- Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya aikewa Atiku wasikar kar-ta-kwana kan raina masa hankali
- Kauran na Bauchi na cikin wadanda suka fafata da Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa
Abuja - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Talata ya zanna da dan takarar kujerar shugaban kasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a Abuja.
Wannan ganawar ta auku ne biyo bayan rahotannin cewa gwamnan na Bauchi ya yi barazanar hannun riga da yakin neman zaben Atiku a 2023.
A jawabin da ya fitar, Gwamnan yace:
"Yau, na jagoranci masu ruwa da tsakin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Bauchi zuwa wajen dan takaran kujerar shugaban kasa PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a Abuja."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abubuwan da muka tattauna a kai sun hada da cigaban jam'iyyarmu."
Gwamna Bala ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.
Gwamnan Bauchi Ya Aikewa Atiku Muhimmin Sako
Sabbin matsaloli na ƙara kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP, bayan gwamnonin G-5, ƙarƙashin gwamnan Ribas, Nyesom Wike, gwamna Bauchi, Bala Muhammed, yace ba'a kyauta masa ba.
Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnan ya ce ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya maida shi saniyar ware a kwamitin kamfe (PCC).
Da yake nuna fushinsa, Muhammed ya yi zargin cewa Atiku ya yi barazanar hukunta shi sakamakon gogayya da shi a zaɓen fidda gwanin PDP da ya gudana a watan Mayu.
Ƙorafin da gwamnan ya rubuta a wasikar
"An watsar da ni a gangamin yakin neman zaɓen da PCC ya shirya a Kaduna, wanda aka zauna da ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki da manyan arewa da suka wakilci ƙungiyoyin daban-daban,"
"Yayin da Atiku da yan koransa ke kokarin hukunta ni saboda kawai na yi gogayya da shi a zaɓen fidda gwanin PDP, su mutanen da suka zagaye Atiku masu ikirarin suke naɗa sarki na kokarin mun zagon kasa."
"Saboda na ƙi miƙa wuya ga son ransu. Tawagar karshe dake fafutukar ganin bayan Bala, 'Bala Must Go' su ne waɗanda tarihinsu ya goge sakamakon dumɓin nasarori da ayyukan alherin gwamnatin PDP a Bauchi."
Asali: Legit.ng