Babu Dan Majalisa Ko Ministan Da Ke Daukan Albashin N1m A Wata, Gwamnatin Tarayya

Babu Dan Majalisa Ko Ministan Da Ke Daukan Albashin N1m A Wata, Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa albashin yan majalisa da Ministoci ya yi kadan a wata
  • Shugaba Buhari ya umurci hukumar RMAFC su zauna don duba idan akwai bukatan gyara
  • Shugaban hukumar yace yan Najeriya su daina tunanin yan siyasa na samun wani albashin kwarai

Babu dan majalisa ko Minista da ke daukan albashin sama da naira milyan daya a wata, Shugaban hukumar kasafta albashi da kudin shiga RMAFC, Mohammed Bello Shehu.

Shugaban na RMAFC ya bayyana hakan a hirar Talabijin, rahoton TheNation.

Ya karyata rahoton cewa zaman nazari kan albashin da aka shirya kari za'a yi wa yan siyasa.

Buhari
Babu Dan Majalisa Ko Ministan Da Ke Daukan Albashin N1m A Wata, Gwamnatin Tarayya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Akwai kura-kuran da muka yi, shi yasa muka shirya yin haka yanzu, ba gaskiya bane maganar cewa muna kokarin baiwa shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisa makudan kudade kyau."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daga Karshe, Ngige ya bayyana dalilin biyan Malaman Jami'a rabin albashi

"Kuma mutane su daina tunanin yan majalisa da sanatoci na samun wani kudi mai yawa, ba haka bane; babu dan majalisa, babu sanata, babu ministan dake daukan sama da milyan daya a wata a Najeriya."

Yace shugaba Muhammadu Buhari ya basu umurnin nazari kan albashin Alkalai sai suka yanke shawarar yi na kowa gaba daya.

Ba Zai Yiwu Mu Biya Lakcarori Kudin Aikin Da Basu Yi Ba, Ngige

A wani labarin kuwa, Ministan Kwadago da Aikin, Chris Ngige, Yi ya watsi da rahotannin cewa ya saba alkawarin da yayi da ASUU biyo bayan biyan albashin rabin wata wa Malaman Jami'a.

A jawabin da mai magana da yawun ma'aikatar kwadago, Olajide Oshundun, ranar Asabar, yace babu gaskiya cikin zargin da ake masa, rahoton Tribune.

Yace albashin da aka biya Malaman ASUU na ranakun da suka yi aiki ne a watan Oktoba kuma ba rabi ba kamar yadda ake radawa.

Kara karanta wannan

Sai Ta An yi Addu'a, Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye

A cewarsa, ba zai yiwu a biyashi kudin aikin da basu yi ba.

Kungiyar Malaman Jami’a Ta ASUU Na Shirin Komawa Yajin Aiki

Yayin da daliban jami'a ke tsaka da doki da murnar komawa makaranta bayan watanni takwas suna zaune a gida saboda yajin ASUU, kungiyar ta ce za ta sake shiga yajin aiki.

Wannan na zuwa ne kasa da wata guda da kungiyar ta janye yajin aikin da ta fara tun watan Fabrairun bana, kamar rahotanni a baya suka bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel