Ya Kamata A Saka Hoton Obasanjo A Sabbin Kudaden Da Za'a Buga, Atiku

Ya Kamata A Saka Hoton Obasanjo A Sabbin Kudaden Da Za'a Buga, Atiku

  • Alhaji Atiku Abubakar ya bada shawaran a baiwa tsohon maigidansa Obasanjo kyautar Nobel
  • Atiku yace ko ba komai ya kamata shugaba Buhari ya sanya hoton Obasanjo a sabon takardan Naira da za'a buga
  • Cif Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya sau biyu a rayuwarsa; lokacin mulkin Soja da lokacin demokradiyya

Dan takaran kujerar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bukaci a sanya hoton Obasanjo cikin sabon sauyin da za'a yiwa Naira.

Cif Olusegun Obasanjo dai tsohon shugaban kasan Najeriya ne wanda yayi mulki tsakanin 1999 da 2007.

Atiku a jawabin da ya fitar ranar Asabar a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa allai Obasanjo mutumin kirki ne kuma mai son zaman lafiya saboda ya cancanci a jinjina masa.

Wannan ya biyo bayan sulhun da Obasanjo da yayi tsakanin yakin da auku tsakanin gwamnatin kasar Habasha da yan tawayen Tigray da aka kwashe shekaru biyu ana gwabzawa.

Kara karanta wannan

Buhari Na Shirin Kashe Biliyan 2 Domin Sabunta Motocin Aso Villa

An fara wannan yaki ne ranar 4 ga Nuwamba, 2022 lokacin da shugaban kasan Habasha, Abiy Ahmed, ya tura jami'an yaki cikin Tigray.

Atiku Obasanjo
Ya Kamata A Saka Hoton Obasanjo A Sabbin Kudaden Da Za'a Buga, Atiku Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Ko kadan ban yi mamaki ba. Na san mai gidana. Ya taba irin haka tsakanin Laberiya da São Tomé lokacin muna mulki."
"Ko ba komai, ya cancani a basa kyautar Nobel na zaman lafiya, kuma zan bada shawaran haka irin aka fara rijista."
"Wannan mutumi ne ya kamata a sanya hotonsa cikin sabon Nairan da za'a sauya don zaburar da yan gobe don sanin irin sadaukar da kan da ya yiwa kasarsa da nahiyar gaba daya."

Zaben 2023: Aikin Atiku Shine Haɗa Kan Najeriya Ba PDP Ba, In Ji Anenih

A wani labarin, Mamban kwamitin yakin neman zabe shugaban kasa na Atiku Abubakar, Ose Anenih, ya ce aikin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta Peoples Democratic Party, PDP, shine hada kan Najeriya, ba jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

Ose Anenih ya bayyana hakan ne yayin hira da shi da aka yi a shirin Politics Today na Channels Television

Dan marigayin jigon PDP, Cif Tony Anenih, ya ce dauyin hada kan jam'iyya ya rataya ne kan shugaban jam'iyyar na kasa da kwamitin gudanarwa na kasa, NWC.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida