Rikici Ya Barke A Jam'iyyar PDP, An Fitittiki Dan Takaran Gwamnanta A Jihar Ogun

Rikici Ya Barke A Jam'iyyar PDP, An Fitittiki Dan Takaran Gwamnanta A Jihar Ogun

  • Da yiwuwan ayi zaben gwamnan jihar Ogun a Maris 2023 ba tare da jam'iyyar adawa ta PDP ba
  • Jam'iyyar maimakon dinke barakarta ta sallami manyan jiga-jigan jam'iyyar ciki har da dan takarar gwamna
  • A jerin yan takaran kujerar gwamna a zaben 2023 na jihar Ogun da INEC ta fitar, babu sunan na PDP

Rikicin da ya 'dai'daita jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun ya kara muni ranar Alhamis yayinda jam'iyyar ta fitittiki dan takaran gwamnanta, Ladi Adebutu da wasu mutum hudu.

Jam'iyyar ta ce ta sallamesu ne saboda an kamasu da magudin sunayen Deleget da akayi amfani wajen zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar da kuma saba doka.

An gudanar da zaben ne ranar 25 ga watan Mayu, 2022 kuma Ladi Adebutu ya lashe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Wadanda jam'iyyar ta sallama a yau sun hada da Taiwo Akinlabi, Sunday Solarin, Kayode Adebayo da Akinloye Bankole, rahoton TheNation.

Shugaban kwamitin ladabtar da su, Hon. Akintunde Mufutau, a jawabin da aka fitar yace:

"Bayan kyakkyawan dubi cikin zarge-zargen da ake musu, kwamitin ta tabbatar suna da kashi a gindi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka, an bada shawaran sallamarsu."
Jam'iyyar PDP
Rikici Ya Barke A Jam'iyyar PDP, An Fitittiki Dan Takaran Gwamnanta A Jihar Ogun
Asali: UGC

Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Katsina, Tsagi Daya Ya Dakatar da Dan Takarar Gwamna

A jihar Katsina kuwa, jam'iyyar adawa ta PDP ta sake shiga dambarwa biyo bayan wani yunkuri mai cike da ruɗani na tsige shugaban jam'iyya, Alhaji Yusuf Salisu Majigiri.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya ƙara tsananta yayin da ake zargin cewa an dakatar da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023, Yakubu Lado Ɗanmarke.

Tsagin ɗan takara, Lado Ɗanmarke, ya haɗa tawagar shugabannin PDP na wasu kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki suka yanke cewa ba zai yuwu a bar kujerar shugaba hannun Majigiri ba, wanda ke neman takarar majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Zabi Babban Jiha A Arewa Don Kadamar Da Kamfen Dinsa Na 2023

Bugu da ƙari, suna zargin cewa Majigiri, wanda ke samun goyon baya daga tsohon gwamna, Ibrahim Shehu Shema, na kokarin cin dunduniyar ɗan takarar gwamna ta bayan fage.

Wata majiya a PDP tace sakamakon haka tsagin Lado suka taru suka tunbuke Majigiri daga kujerar shugaba kana suka zaɓi mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar Daura, Alhaji Lawal Danbaci, a matsayin muƙaddashin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida