Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Yan Gudun Hijra

Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Yan Gudun Hijra

  • Yan ta'addan Boko Haram sun fara kai hare-haren sansanin yan gudun hijra suna satan kayan abinci
  • Wadannan yan ta'adda ne suka yi sanadiyar guduwan wadannan mutane daga muhallansu na asali
  • Najeriya, Chadi da Nijar na fama da rikicin Boko Haram kuma miliyoyin mutane sun rasa rayukansu

NGagala - Yan ta'addan Boko Haram sun kai mumunan hari sansanin yan gudun Hijra inda suka hallaka mutane kuma suka kona gidaje tare kwashe kayan abinci.

Masanin harkokin tsaro a yankin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Alhamis.

A cewarsa akalla mutum hudu sun rasa rayukansu yayinda aka kona gidaje tare da sace kayan abinci a shaguna a sansanin gudun Hijra dake Nijar.

Yace harin ya auku ne da daren Laraba, 2 ga watan Nuwamba, 2022.

Kara karanta wannan

Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

Yace:

"Akalla mutum hudu, maza biyu da mata biyu aka kashe, an kona gidaje da dama kuma an sace kaya a shaguna...wasu sun jikkata."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun shiga sansanin ne dake NGagala Peulh...misalin karfe 10 na dare kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi."
"Wadanda suka jikkata an kaisu asibitin NGuimi."

Fatara Da Talauci Na Iya Sa Wadanda Ke Sansanin Gudun Hijira Shiga Boko Haram

A wani labarin, Gwamna Jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana fargaba kan karancin kudi da fatara, idan ba a magance shi ba, na iya tilasta wasu mutanen da ke sansanin gudun hijira shiga Boko Haram ko ISWAP.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin rufe sansanin yan gudun hijira na Dalori-1, Dalori-2 Gubio da Muna a Maiduguri, ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da ajiye mutanenta a sansanin yan gudun hijirar ba.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Ya ce jihar, a karkashin jagorancinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an mayar da mutane gidajensu cikin mutunci.

Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyayensu, Ya Dauko Marayu, Zai Kashe Masu N300m

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada sanarwar tallafin kudin karatu ga marayun da suka rasa iyayensu a yakin Boko Haram.

Hukumar dillacin labarai ta kawo rahoto cewa Mai girma Gwamnan zai biya N300m domin ‘ya ‘yan ‘yan kato-da-gora su samu damar yin karatun zamani.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida