Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

  • Tun da Gwamnan CBN ya sanar da cewa za a sauya fasalin takardun kudi, darajar Naira take cigaba da fadi a kasuwar canji
  • Mutane da ake zargi da boye Naira suka rika fito da Nairori domin su canza su da kudaden kasar waje kafin karewar wa'adin wata 3 da aka bada
  • Hukumar EFCC kuwa ta fara kai hari shagunan yan canji suna auba ido kan abubuwan dake faruwa

Kano - An damke yan kasuwar canji akalla takwas a jihar Kano sakamakon samamen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kai kasuwar.

DailyTrust ta ruwaito cewa jami'an na EFCC sun dira wajen ne da yammacin Talata cikin motoci takwas cike da jami'an tsaro.

Wannan ya biyo bayan harin da EFCC ta kai kasuwar yan canji a Abuja.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

Daya daga cikin yan canjin wanda ya bukaci a sakaye sunansa kafin zuwansu wasu yan canji sun ankare kuma sun rufe shagunansu gudun kada abinda ya afkawa yan Abuja ya afka musu.

EFCC.
Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani dan canjin yace:

"Duk lokacin da suka kawo hari wannan kasuwar, farashin Dala na tashi. Misalin yau, (Laraba) Dalar Amurka ta tashi N845 sabanin N835 da aka sayar jiya (Talata) kafin zuwan EFCC."
"Tsadar nan ba laifinmu bane. Gwamnati ce ba ta sakin Dala. Da tsada muke saya, kuma dole mu sayar a hakan don mu samu namu riban."

Rahoton ya kara da cewa wani babban jami'in EFCC wanda ya tabbatar da harin yace sun kai simamen ne don taimakawa gwamnatin tarayya wajen rage tashin da Dalar ke yi.

Yace sun dade suna bibiyan yan canjin kuma barayi na amfani da su wajen boye kudade don tsoron asarar kudadensu biyo bayan sanarwan sauya fasalin Naira.

Kara karanta wannan

CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

Jami'an ya kara da cewa sun damke mutum takwas kan laifin sana'ar canji ba tare da lasisi ba kuma na garkamesu a ofishin hukumar dake Kano inda za'a gudanar da bincike kansu.

Dalar Amurka ta Kara Tsinkewa a Kasuwar Canji, N800 Ba Za Ta Iya Sayen $1 ba

Darajar Naira tana cigaba da sauka kasa ne kamar yadda cinikin da ake yi a kasuwar canji suka tabbatar a farkon makon nan.

A wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar 1 ga watan Nuwamba 2022, an ji cewa Dalar Amurka tana cigaba da yin riba a kan Naira.

A ranar Litinin dinnan, sai da ‘yan canji suka saida Dalar Amurka daya a kan N815 a garin Legas, kusan abin da ba a taba jin labari ba.

Lamarin ya fi haka jagwalgwalewa a birnin tarayya Abuja, domin ‘yan canji sun saida $1 a kan N818 kafin a tashi daga kasuwa a Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida