Da Duminsa: An Hana Jirage Tashi Yayin da Ma’aikata Suka Rufe Inda Jirage Suke a Legas

Da Duminsa: An Hana Jirage Tashi Yayin da Ma’aikata Suka Rufe Inda Jirage Suke a Legas

  • Ma’aikatan filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas sun rufe wurin tashin jiragen sama na biyu dake filin jirgin a safiyar Talata
  • Wannan ya biyo bayan zanga-zangar lumana da suka balle da sassafe kan korar wasu daga cikin ma’aikata 34 da aka yi na kungiyarsu
  • Kamar yadda aka gano, dole ta da aka dakatar da tashi da daukar jiragen saman har sai yadda ta kama, lamarin da ya tada hankalin fasinjoji

Legas - An dakatar da tashin jiragen safe yayin da aka bar fasinjoji cikin damuwa sakamakon rufe filin sauka da tashin jiragen sama da Murtala Muhammad dake Legas da aka yi a safiyar Talata.

Murtala Muhammad
Da Duminsa: An Hana Jirage Tashi Yayin da Ma’aikata Suka Rufe Inda Jirage Suke a Legas. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, ma’aikatan filin jirgin suna zanga-zanga kan korar wasu mambobin Bi-Courtney Aviation Services Limited da aka yi ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mambobin Kungiyar ma’aikatan sufurin sama ta Najeriya a ranar Talata sun rufe hanyar shiga wurin jiragen sama na biyu a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas kan korar ma’aikata 34 daga aiki.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, lamarin ya hana jiragen sama kamar na kamfanonin Ibom Air da Air Peac tashi a filin jirgin saman.

A bayanin da Ibom Air ta aikewa fasinjojin, tace matakin da ma’aikatan kungiyar suka dauka zai matukar taka rawa wurin hana su ayyuka a ciki da wajen Legas a yau.

“Muna takaicin abinda matakin ba-Zara da kungiyar ta dauka yau zai yi a kan shirye-shiryenmu na yau. Muna kira gareku da ku kasance kusa da dukkan kafofin sadarwarku domin samun bayanai.”

- Kamfanin jirgin saman yace.

A takardar yajin aikin da ATSSSAN ta bayar, wadanda korar aikin ta ritsa dasu sun hada da shugaban reshen, sakatare, ma’aji da shugaban mata wadanda suka bukaci a biya ma’aikatan da suka bar aiki hakkinsu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kama mata da miji dake safarar mutane a wata jiha

Kungiyar tace hukumar BASL ta dauka wannan matakin ne yayin da dukkan bangarorin biyu ke sasanci yadda za a biya hakkin.

Ta duba hukuncin na da sauke haushi kan mambobinta da shugabannin dake kokarin sauke hakkin dake kansu.

Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

A wani labari na daban, Fasinjoji da dama ciki har da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun tsallake rijiya da baya a yayin da jirgin Max Air da ya tashi daga Kano zai tafi Abuja ya samu matsalar inji mintuna 10 bayan tashi daga filin jirgin Kano, MAKIA.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa jirgin na Max Air mai lamba VM1645 wanda ya kamata ya tashi karfe 1.30 na rana amma aka yi jinkiri mintuna 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: