Mota mai tuka kanta ta kashe wata mata a garin Tempe

Mota mai tuka kanta ta kashe wata mata a garin Tempe

- Motar ta kamfanin Uber tana cikin yanayin saiti na tuki da kanta, tare da Direba a ciki, lokacin da ta buge wata mata mai tafiya a gefen titi

- An kwantar da matar a asibiti, amma daga baya ta mutu sakamakon raunnikan da taji

- Kamfanin na Uber ya dakatarda yin amfani da mota mai tuka kanta don gwaji ko tuka abokan kasuwanci a garuruwan Tempe, Pittsburgh, Toronto, da kuma San Francisco na kasar Amurka

Motar ta kamfanin Uber tana cikin yanayin saiti na tuki da kanta, tare da Direba a ciki, lokacin data buge wata mata tana tafiya a gefen hanya, a garin Tempe da yammacin ranar Lahadi, cewar kamfanin dake a garin na San Francisco na kasar Amurka.

Mota mai tuka kanta ta kashe wata mata a garin Tempe
Mota mai tuka kanta ta kashe wata mata a garin Tempe

Matar ta kwanta a asibiti, kafin daga baya ta mutu sakamakon raunukan da ta samu. Kamfanin na Uber ya dakatarda yin amfani da mota mai tuka kanta, don gwaji ko tuka abokan kasuwanci a garuruwan Tempe, Pittsburgh, Toronto, da San Francisco kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

KU KARANTA: Allah ya yiwa shugaban makarantar sakandire mafi dadewa a aiki rasuwa

Tempe, na daya daga cikin garuruwa na hanyar Pittsburgh, inda kamfanin motar ke amfani da motar mai tuka kanta don safarar mutane zuwa wuraren harkokinsu na yau da kullun.

Mai kula da motar wanda ke zaune a kujerar direba, shi kadai ne a cikin motar lokacin da wannan al’amari ya auku, inji kamfanin na Uber. Motar tana hannun ‘yan sanda a ranar Litinin. Hatsarin na ranar Lahadi, shine karo na farko da motar mai tuka kanta ta samu da masu tafiya a gefen hanya.

Hatsari na farko da mota mai tuka kanta tayi a shine a tsakiyar shekarar 2016, kuma ya shafi mota mai kirar Tesla.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164