Sheikh Gumi Ya Soki Sauya Takardun Kudi, Ya Kwatanta Hakan da Halaka Kai

Sheikh Gumi Ya Soki Sauya Takardun Kudi, Ya Kwatanta Hakan da Halaka Kai

  • Fitaccen Malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki hukuncin gwamnatin tarayya ba sauya wasu takardun Naira
  • Ya sanar da cewa kashi 80 na ‘yan Najeriya suna amfani ne da tsabar kudi wurin siye da siyarwa, sauya kudi kuwa zai talauta su ne da kawo fatara
  • Gumi yace a bangaren shawo kan matsalar garkuwa da mutane, hakan zai sa su tsira karbar kudin fansa a dala ko kudaden kasashen ketare

Kaduna - Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki kokarin babban bankin Najeriya na sauya wasu takardun Naira inda ya kwatanta lamarin da halaka kai ta fannin tattalin arzikin ‘yan Najeriya balle mazauna kauye.

Sheikh Ahmad Gumi
Sheikh Gumi Ya Soki Sauya Takardun Kudi, Ya Kwatanta Hakan da Halaka Kai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, kamar yadda yace, kashi 80 na ‘yan Najeriya mazauna kauye ne kuma sun dogara da tsabar kudi domin siye da siyarwa.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa

Gumi yace duk wani tsari da zai mitsike zagayawar kudi tsabarsu zai zama tamkar ibtila’i ga kasar.

Ya kara da yin bayanin cewa tsarin ba zai taba hana masu garkuwa da mutane kudi tsabarsu ba saboda zasu iya yanke hukuncin karbar kudin fansa a dala da sauran kudaden ketare kuma hakan ya matsantawa rayuwar jama’a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mutanen dake siyar da kayayyaki zasu fada maka cewa da yawan ‘yan Najeriya basu da kudi, don haka ‘yan kasuwa suna ta tafka asara. A wannan wurin duk abinda zai kawo tsaiko ga yawon kudi zai zamo ibtila’i a kasar nan.
“Da yawan hukunci masu kyau ana aiwatar dasu ne a lokacin da bai dace ba. Akwai yuwuwar wannan zai kasance wani. Duk dai yadda wadanda suka kawo tsarin zasu kuranta shi, amfanin dai ba kamar yadda ake tsammani bane tunda halin da ake ciki na bayyana rashin dacewa Daga bisani.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

“Kashi 80 na ‘yan Najeriya musamman ‘yan kauye suna amfani da tsabar kudi ne. Fannin kwatsam na komawa amfani da kudin da ba tsaba ba yana nufin karuwar talauci a cikin kankanin lokaci.
“Wannan shirin ba na gwamnati bane dake iya bakin rai. Idan da akwai amfanin irin hakan, yana zuwa ne bayan shekaru masu yawa na matsanancin talauci da matsin rayuwa wanda babu gwamnati mai fatan alheri da ya dace ta mika mulki a hakan.
“Da a ce an fara tun 2015, hakan na iya zama daidai tunda gwamnatin ce zata dandana kudarta kan hakan. Mu shaida ne kan hana achaba, siyar da fetur da datse sadarwa a jihohin da ‘yan bindiga suke cin karensu babu babbaka. Hakan bai shawo kan komai ba sai dai azabtar da jama’a.
“Wannan na nuna cewa gwamnati bata duba komai na hukuncinta masu matsala.”

- Shehin Malamin yace.

Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

A wani labari na daban, babban bankin Najeriya, CBN ta bi dukkan matakan da suka dace wurin sabunta takardun naira uku da zai yi, Daily Trust ta rahoto.

Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya sanar da hakan yayin martani ga Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed, wacce tace ma’aikatar ta bata da masaniya kan sabon tsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng