Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 21 da ‘Yan Bindiga Suka Sace
- ‘Yan Sanda a jihar Katsina sun ceto wasu mutum 21 da suka hada da mata 15 da yara 6 daga hannun ‘yan bindiga bayan an yi garkuwa dasu
- SP Gambo Isah ya sanar da cewa, ‘yan sandan sun samu kiran gaggawa daga kauyukan Buraji da Sabon Sara kan cewa an kwashe jama’a
- ‘Yan sandan sun tare hanyar fita kauyukan inda suka budewa ‘yan bindigan wuta har suka halaka wasu yayi da wasu suka tsere da raunikan bindiga
Katsina - Jami’an ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a sun ceto mutum 21 da aka yi garkuwa dasu da suka hada da mata 15 da kananan yara 6 a karamar hukumar Dutsin Ma ta jihar Katsina, Channels TV ta rahoto.
An ceto su wurin karfe 4:30 na asuba bayan rundunar ‘yan sandan sun samu kira gaggawa kan cewa ‘yan ta’adda da yawansu a kan babura sun kai farmaki inda suka dinga harbe-harbe a kauyukan Buraji da Sabon Sara.
Bayan samun bayanin, kwamandan yankin Dutsin Ma, Mohammed Makama, ya jagoranci ‘yan sanda inda suka datse hanyar fita kauyen Gandun Sarki inda suka yi arangama tare da fito na fito inda cike da nasara aka ceto wadanda aka sacen.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah a takardar da ya fitar yace an kashe da yawa daga cikin ‘yan ta’addan kuma sauran sun tsere daga wurin da raunikan bindiga.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kara da cewa tawagarsu tana cigaba da kakkabe yankin tare da fatan samo gawawwaki da kuma damke wadanda suka tsere da raunika yayin da ake cigaba da bincike.
Yadda Jami’an ’Yan Sanda Suka Ceto Wasu Mutanen da Aka Yi Garkuwa Dasu a Jihar Kwara
A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta ceto mutum hudu daga cikin mutane shida da aka sace a babbar hanyar Obbo-Ile da Osi a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Okasanmi Ajayi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata 16 ga watan Agusta a Ilorin, Premium Times ta ruwaito.
Ya bayyana cewa, jim kadan bayan samun labarin abin da ya faru, jami'an 'yan sanda, 'yan banga da mafarauta sun dura wurin da lamarin ya faru domin gano tushen lamarin.
Asali: Legit.ng