Nnamdi Kanu: Buhari Ba Ya Girmama Ibo, In Ji Ɗan Takarar Majalisa Na PDP

Nnamdi Kanu: Buhari Ba Ya Girmama Ibo, In Ji Ɗan Takarar Majalisa Na PDP

  • Mr Ikenga Ugochinyere, dan takarar majalisar tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Abia ya ce Shugaba Buhari bai girmama Ibo
  • Ugochinyere ya bayyana hakan ne biyo bayan kin sakin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, da ya ce Buhari ya ki yi duk da cewa kotu ta bada umurnin sakinsu har sau uku
  • Dan takarar na PDP ya ce hakan ba komai bane illa kiyayya da rashin girmamawa, ya kuma yi kira ga Ibo su juya wa APC baya saboda abin da Buhari ke wa Ibo

Abia - Dan takarar jam'iyyar PDP na mazabar Ideato a Jihar Imo, Ikenga Ugochinyere, a ranar Juma'a, ya ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari, biyo bayan cigaba da tsare shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, duk da kotu ta bada umurnin sakinsa sau uku.

Kara karanta wannan

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Kotun daukaka kara a Abuja ta bada umurnin sakin Kanu kan zargin ta'addanci da aka shigar a kansa, The Punch ta rahoto.

Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu: Buhari Ba Ya Girmama Ibo, In Ji Ɗan Takarar Majalisa Na PDP. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Babban kotun tarayya, a Umuahia, ita ma ta bada umurnin a saki Kanu, ta umurci gwamnatin tarayya ta mayar da shi Kenya inda aka dako shi ba bisa ka'ida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban kotu a Abia ita ma ta yanke hukunci na sakin shugaban na IPOB.

Ugochinyere, wanda shine kakakin 'Coalition of United Political Parties cikin wani sanarwa, ta ce cigaba da tsare Kanu duk da umurnin kotun ya nuna cewa gwamnati ba ta girmama doka.

Ya kara da cewa lamarin hujja ne da ke nuna Shugaba Buhari bai ganin mutane Ibo da kima.

A cewarsa, yan takarar jam'iyyar APC a kowanne mataki za su gamu da sakamakon kiyayyar da Buhari ke yi wa Ibo, da Ideato da mutanen Imo.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu Ya Shigar da Karar Gwamnatin Buhari, Yana Neman a Biya Shi N100bn

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Abin mamaki ne ganin yadda Shugaban kasa zai rika lamuntar abin da mutanensa da hukumomi ke yi na saba doka duk da cewa ya sha furtawa a fili cewa kotu ce za ta yanke hukuncin abin da zai faru da Kanu.
"Matakin wannan gwamnatin cin mutunci ne ga ibo, musamman sarakuna da shugabannin addini wadanda suka tuntubi Buhari sau da yawa kan batun Kanu, amma ya dage cewa hurumin kotu ne."

Ta cigaba da cewa:

"Wannan kiyayya ne da kin jinin Ibo daga shugaban kasa da gwamnatinsa kuma bai kamata a kyalle ba tare da Igbo sun bada amsa da zai nuna fushinsu.
"Don haka na yi kira ga Igbo su bawa Buhari amsa ta hanyar juyawa dukkan yan takarar APC baya.
"Kada Ibo su bawa yan takarar APC ko da kuri'a daya ne daga sama har kasa don nuna fushinsu ga gwamnati.
"Gwamnati da bata girmama Ibo da shugabanninta bai kamata a saka mata da kuri'a ba."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164