‘Dan Sanda Ya Sokawa Abokin Aikinsa Almakashi Yayin da Suke Baiwa Hammata Iska
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kama wani jami’inta da ya sokawa abokin aikinsa almakashi inda ya sheka lahira
- Kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyana, wata hayaniya ce ta hada jami’an biyu har ta kai su ga ba hammata iska
- An damke jami’in da yayi kisan kan inda aka mika shi sashin binciken na musamman da kuma kisan kai a jihar Kebbi
Kebbi - Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi tace Shu’aibu Sani Malumfashi, daya daga cikin jami’anta ya sheka lahira bayan abokin aikinsa mai suna Abdullahi Garba, ya soka masa almakashi.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayyana, Nafiu Abubakar, mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis.
Abubakar yace Abdullahi Garba, wanda ake zargin, shi ne jami’in dake lura da caji ofis din Sauwa kuma sun samu hargitsi ne da Sani Malumfashi, mamacin, wanda ke matsayin jami’in kula da laifuka a hedkwatar ‘yan sanda ta Argungun.
Yace jami’an sun ba hammata iska bayan muhawarar da ta sarke a tsakaninsu a shagon wanda ake zargin ranar 19 ga watan Oktoba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A sakamakon hakan, sun ba hammata iska a gaban shagon Abdullahi Garba.”
- Yace.
“A yayin da ake tsaka da damben, ASP Abdullahi Garba ya sokawa ASP Shu’aibu Sani-Malumfashi a hakarkarinsa na hagu da almakashi.
“Bayan samun rahoton, DPO din Argungun ya hanzarta zuwa wurin inda ya kama jami’in da ake zargi.
“An hanzarta kai ASP Shu’aibu Sani Malumfashi zuwa asibitin Sir Yahaya Memorial dake Birnin Kebbi inda cike da takaici ya rasa ransa.
“A halin yanzu, an kama ASP Abdullahi Garba kuma an garkame shi a sashen binciken sirri na Birnin Kebbi.
“An kara da mika lamarin sashen kisan kai domin bincike don gano abinda ya assasa faruwar lamarin.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan yace Ahmed Magaji Kontagora, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, ya bada umarnin bincike kan lamarin dake tattare da kisan kan.
“Hakazalika, kwamishinan ‘yan sandan ya ja kunnen jami’an da a kodayaushe su kasance masu zaman lafiya da juna tare da kai rahoton duk wasu rikicinsu ga sashin da suka dace ba tare da daukan doka a hannu ba.”
- Ya kara da cewa.
Abia: ‘Dan Sanda Ya Bindige Abokin Aikinsa Bayan Rikici Ya Hada su
A wani labari na daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta bayyana yadda ta damko wani ‘dan sanda da ake zargi da bindige abokin aikinsa har lahira.
Marigayin, mai suna Samuel Ugor, mai mukamin sifetan l ‘yan sanda, ya rasa ransa ne sakamakon wata yar hatsaniya.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayyana, ‘yan sandan na aiki ne karkashin Ginger Onwusibe, ‘dan majalisa mai wakiltar kudancin mazabar Isiala Ngwa a majalisar jihar Abia.
Asali: Legit.ng