‘Dan Najeriya Ya Sheka Lahira Yana Tsaka da Holewa da Budurwa a Otal
- Wani ‘dan jihar Ondo ya sheka lahira yayin da yake tsaka da holewa da wata mata a wani otal da yammacin Laraba wurin karfe 9 na dare
- Matar da kanta ta fasa ihu bayan ya yanke jiki ya fadi ya mutu, lamarin da yasa manajan otal din ya kira jami’an ‘yan sanda
- Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da cewa mutuwar farat daya mutumin yayi duk da suna cigaba da bincike
Ondo - Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo tace ta fara bincike kan mutuwar wani mutum da ake zargin ya sheka lahira bayan sun gama gwangwajewa da wata mata a otal a jihar.
An tattaro yadda mamacin mai suna Lanre ya mutu ne yayin suke holewa da wata mata a otal ranar Laraba da yammaci. Har yanzu dai ba a gano ko wacece matar ba, jaridar Punch ta rahoto.
Wata majiya tace:
“Matar da kanta ta bayyana lamarin bayan mutumin ya fadi bayan ya fito wanka wurin karfe 9 na dare da suka kammala sha’aninsu. Hayaniyarta ce ta janyo hankalin manajan otal din wanda ya gayyaci ‘yan sanda daga ofishin Enu-Owa zuwa wurin.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, yayin da aka tuntubeta tace mutuwar farat daya ce kuma ‘yan sanda sun fara bincike.
“Mutuwar farat daya ce. Mun fara bincike kan lamarin.”
- Kakakin rundunar ‘yan sandan tace.
An tattaro cewa tuni aka mika gawar mamacin zuwa ma’adanar gawawwaki ta jami’ar Ondo.
An tsinta gawar magidanci da budurwa a mota, sun mutu suna tsaka da 'kece-raini'
A wani labari na daban, an tsinta gawar wani mutum da wata mata wadanda aka gano sun mutu a cikin mota kirar SUV yayin da suke tsaka da jima'i.
The Nation ta ruwaito cewa, an tsinta gawarsu a daren Lahadi a rukunin gidaje na Jakande da ke Isolo a jihar Legas yayin da makwabta da suka balle motar bayan sun lura da injinta a kunne tun daga ranar Asabar.
Mutumin mai suna Koyejo ya dauka masoyiyarsa wacce ba a san sunanta ba yayin da yake hanyarsa ta zuwa gidan iyayensa da ke rukunin gidaje na Jakande a Isolo kamar yadda abokansa suka yi ikirari.
Asali: Legit.ng