Barazanar Tsaro: IGP Alkali Baba Ya Fitar da Lambobin Kiran Gaggawa ga ‘Yan Najeriya

Barazanar Tsaro: IGP Alkali Baba Ya Fitar da Lambobin Kiran Gaggawa ga ‘Yan Najeriya

  • Shugaban ‘yan sandan Najeriya, IGP Alkali Baba Usman ya bayar da lambobin da ‘yan Najeriya zasu yi wa kiran gaggawa a duk lokacin da aka kai musu farmaki
  • Sifeta janar din na ‘yan sandan Najeriya ya jaddada cewa lambobin suna aiki babu dare babu rana kuma ‘yan sandan Najeriya a shirye suke don kai dauki
  • Ya sanar da cewa babu wata barazanar tsaro a babban birnin tarayyan kasar nan inda ya bukaci jama’a da su cigaba da al’amuransu na yau da kullum

FCT, Abuja - Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, a daren Juma’a ya saki nambobin da za a yi wa kiran gaggawa a fadin kasar nan a duk lokacin da aka samu farmakin ‘yan ta’adda, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu

Alkali Baba Usman
Barazanar Tsaro: IGP Alkali Baba Ya Fitar da Lambobin Kiran Gaggawa ga ‘Yan Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Baba yace ‘yan sandan Najeriya na aiki tare da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiyarsa dukkan jama’a a fadin kasar nan.

Babban ‘Dan sandan ya kara da bayyana cewa, babu wani shirin farmaki a babban birnin tarayya kamar yadda Amurka ta bayyana.

Sifeta janar din ya jaddada hakan yayin da yake kira ga manajojin tsari na rundunar ‘yan sandan Najeriya da su tsananta tsaro a duk inda suke da alhakin hakan ballantana babban birnin tarayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda takardar da kakakin rundunar ‘yan sandan, Olumiyiwa Adejobi ya fitar, sifeta janar din ya bada umarnin cewa dukkan lambobin gaggawa a bude su suna aiki babu dare babu rana.

Adejobi yace ya kara da umarnin cewa jami’an yaki su kasance cikin shiri a kowanne lokaci domin martani ga lamurran gaggawa idan an samu kira.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka, Manyan Kasashen Duniya 3 Sun gano Yiwuwar kai hari a Birnin Abuja

Takardar ta kara da cewa:

“Mazaunan babban birnin tarayya ana kiransu da su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suka zarga ko mutum ga ‘yan sanda ta wadannan layikan: 08032003913, 08061581938, 07057337653, and 08028940883.”

Sifeta janar din yayi kira ga mazauna babban birnin tarayya da su cigaba da lamurransu na rayuwa inda yace duk wani abu da ya dace a yi an yi shi domin magance barazanar.

Baba ya jaddada mayar da hankalin ‘yan sandan Najeriya wurin kawar da dukkan barazana tare da kare rayuka da dukiyoyin mazaunan dukkan kasar.

Amurka Ta Amince Da Ficewar 'Yan Kasarta da Ma'aikatan Ofishin Jakadancinta Daga Najeriya

A wani labari na daban, Gwamnatin kasar Amurka ta amincewa 'yan kasar mazauna Najeriya da su fara fita daga kasar biyo bayan rahoton barazanar tsaro da hukumomin kasar suka samo, Channels Tv ta ruwaito.

A wani sakon ankararwa da kasar ta fitar a ranar Talata 25 ga watan Oktoba da yamma, ma'aikatar Amurka a Najeriya ta yi alkawarin ba da shawarwarin kariya da tsaron gaggawa ga 'yan kasar mazauna Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng