Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

  • Biyo bayan kwashe yan kasarta da Amurka ta fara yi a Abuja, babban kantin sayar da kayayyaki ta rufe shagunanta
  • Gwamnatin tarayya ta ce yan Najeriya su kwantar da hankulansu game da labarin cewa za'a kai hari Abuja
  • Gwamnatin Amurka da ta Burtaniya sun gargadi 'ya'yansu mazauna Najeriya da su kula matuka kan yiwuwar samun hare-hare

Abuja - Babban kantin Jabi Lake Mall dake unguwar Utako a birnin tarayya Abuja ta rufe dukkan shagunanta ranar Alhamis sakamakon barazanar tsaron da ake yiwa garin.

A jawabin da kantin ya daura a shafinsa na Instagram @jabilakemallnigeria, hukumomin sun bayyana cewa duk da cewa ba tada niyyar tadawa mutane hankali, sun yanke shawaran haka ne domin kare rayukan masu zuwa siyayya da ma'aikatanta.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani

Sun kara da cewa suna bibiyan yadda alamarin ke gudana kuma idan komai ya daidaita za'a bude.

Jabi Lake
Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari
Asali: Twitter

A cewar jawabin:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ga dukkan kwastamominmu, zamu rufe Jabi Lake Mall yau, Alhamis, 27 ga Oktoba, 2022."
"Mun yanke wannan shawara ne don kare lafiya ma'aikatanmu da kwastamominmu."
"Muna bibiyan lamarin kuma muna shawara da hukumomin tsaro kuma zamu sanar da ku lokacin da zamu bude."
"Muna ba da hakuri bisa wannan abu, mun gode."

Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa Najeriya ta fi zaman lafiya yanzu fiye da kowani lokaci a shekarun baya-bayan nan.

Lai ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi a taron UNESCO da ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Talata, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

Ya yi martani ne game da gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya tayi na cewa da yiwuwan yan bindiga su kai hari birnin tarayya Abuja.

Ya tuhumci yan jarida da zuzuta lamarin.

Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

Bayanai sun fara bayyana biyo bayan gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya sukayi cewa da yuwuwan yan Boko Haram sun kai hari birnin tarayya Abuja nan ba da dadewa ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun fara basaja da ayyukan hannu cikin birnin tarayya.

Rahoton yace wasu kwamandojin Boko Haram sun saje da jama'a kuma sun kammala shirin kai munanan hare-hare lokaci guda a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida