‘Dan Chana Ya Musanta Halaka Budurwa Ummita a Gaban Kotu

‘Dan Chana Ya Musanta Halaka Budurwa Ummita a Gaban Kotu

  • ‘Dan China Geng Quangron da ake zargi da shiga har gida ya sokawa budurwarsa wuka a sassan jikinta har ta rasa rants, ya musanta aikata hakan
  • A zaman kotun da aka yi a jihar Kano, an karantowa ‘dan Chanan laifin da ake zarginsa da shi inda a take ya musanta aikatawa
  • A take lauyan masu kara ya bukaci a dage sauraron karar zuwa watan Nuwamba lokacin da zasu gabatar da shaidunsu a gaban kotu

Kano - ‘Dan kasar China da ya halaka Budurwarsa a jihar Kano mai suna Ummulkulsum Sani Buhari, Geng Quangron, ya dire gefe yace bai kashe budurwarsa ba.

‘Dan Chana
‘Dan Chana Ya Musanta Halaka Budurwa Ummita a Gaban Kotu. Hoto daga @bbchausa
Asali: Twitter

Geng ya sanar da hakan a babbar kotun jihar Kano mai lamba 17 dake titin Miller a yayin da aka cigaba da sauraren shari’ar da gwamnatin Kano ta shigar.

Kara karanta wannan

Bayan Sauya Sheka, Tsohon Sakataren Katsina Ya Bukaci Mutane Su San Yan Takarar da Zasu Zaba a 2023

Ana zargin Geng da sokawa Ummita wuka wanda hakan yayi ajalinta bayan shigarsa har cikin gidansu dake Unguwar Janbulo, Aminiya ta rahoto.

Abinda ya Faru a Zaman Da Ya Gabata

An samu tsaiko a shari’ar saboda rashin mai fassara a zaman da ya gabata saboda hakkin wanda ake zargi ne ya fahimci abinda ake yi da harshensa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai a zaman kotun na ranar Alhamis, mai gabatar da kara, Barista Musa A. Lawan wanda shi ne kwamishinan shari’ar jihar Kano ya bayyana wanda zai yi fassarar da Guo Cumru ‘dan asalin kasar China.

Barista Lawan ya sanarwa kotun cewa Ofishin Jakadancin Kasar China dake nan Najeriya ne ya samar da wanda zai yi tafinta.

Mai gabatar da kara ya karanto takardar karar kamar Haka:

“A ranar 16 ga Satumba, Geng dake zaune a Unguwar Railway a Kano ka je wani gida dake Janbulo inda ka halaka budurwa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari, ta hanyar caccaka mata wuka a sassan jikinta.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Fito Ta Fadawa Kotu Asalin Dalilin Cigaba da Tsare Nnamadi Kanu

“Laifin yaci karo da sashe na 221 na kundin fenal kod.”

Wanda ake zargi ya musanta aikata laifin

Amma wanda ake zargin a take ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Mai gabatar da karar ya bukaci kotun da ta dage sauraron shari’ar zuwa ranakun 14 da 16 ga Nuwamba don gabatar da shaidu.

Lauyan wanda ake tuhuma,Barista Muhammad Balaraba Danazumi bai aminta da ranakun da aka bukata ba kuma ya shaidawa kotu basu yi masa daidai ba.

Mai gabatar da kara ya roki kotun da tayi la’akari da cewa tafinta na zuwa ne daga Abuja.

Alkali Sanusi Ado Ma’aji ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16, 17 da 18 ga watan Nuwamban 2022.

Ummita: Kotu ta Dage Sauraron Shari'ar 'Dan Chana da Ya Halaka Budurwarsa Saboda Rashin Tafinta

A wani labari na daban, wata babbar kotu dake zama Kano mai lamba 17 dake zama a titin Miller karkasin jagorancin Mai shari'a Saunusi Ado Ma'aji ya dage sauraron shari'a Geng Quangrong, 'dan kasar Chana da ake zargi da halaka budurwasa 'yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: