‘Yan Sanda Sun Damke Matasa 4 Dake Kwacen Ababen Hawa Tare da Siyar da Sassansu
- Rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun yi caraf da wasu mutum 4 da ake zargi da kwarewa wurin kwacen ababen hawan jama’a a yankin Iganmu
- A bayanin da suka yi, suna kwace ababen hawan tare da tarwatsa su sannan su siyar dasu matsayin safaya ga dillalan kasuwar Ladipo
- Dubunsu ta cika ne bayan da suka kwace motar wata mata mai suna Sandra wacce suka fara cire sasanta suna siyarwa amma aka damko su
Legas - Jami’an ‘yan sandan ofishin Ijora Badia na jihar Legas sun damke wasu mutum hudu da ake zargi da kwarewa wurin satar ababen hawa tare da tarwatsa su suna siyar da su matsayin safaya, Daily Trust ta rahoto.
Wadanda ake zargin a bayanin da suka yi, sun zargi cewa da yawa daga cikin dillalansu suna fitacciyar kasuwar Ladipo a yankin Mushin dake jihar.
“Muna tarwatsa da yawa daga cikin ababen hawan da muka kwata daga jama’a. Muna kiran su da Ngbuka. Muna siyar dasu ga dillalai a Ladipo.”
- Ganiyu, daya daga cikin wadanda ake zargin yace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Alafia Afiwajuomo, Ganiyu Tajudeen, Olamilekan Hassan da Lucky Esomojumi.
Hundeyin yace an kama wadanda ake zargin a karkashin gadar Igami bayan tsananin bincike da bayanan sirri da aka tattaro.
“A ranar 29 ga watan Satumban 2022, wadanda ake zargin sun kwace mota kirar Toyota Camry daga wata Sandra a yankin Iganmu dake Surulere a jihar Legas.
“Ana aikin farfasa motar ne yayin da aka kama su kuma aka karbeta. An samo wasu sassan motar da ake zargin an cire tare da siyar dasu matsayin safaya.”
-Yace.
‘Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Samo Kudin Fansa N8.4m a Bauchi
A wani labari na daban, wasu da ake zargi da zama masu garkuwa da mutane har su biyu sun sheka lahira sakamakon musayar wuta ne da suka yi da jami’an ‘yan sanda a kauyen Maina-Maji dake karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Har ila yau, ‘yan sandan sun damke wani matashi mai shekaru 20 mai suna Abubakar Isah da zargin garkuwa da mutane dauke da N8.4m da ake zargin kudin fansa ne ya karba daga jama’a.
Asali: Legit.ng