Bidiyon Budurwa da ta Kone Kwalin Digirinta Bayan Shekaru 4 Tana Neman Aiki

Bidiyon Budurwa da ta Kone Kwalin Digirinta Bayan Shekaru 4 Tana Neman Aiki

  • Wata budurwa ‘yar kasar Malawi ta kakkabo kwalin shaidar digirinta inda ta banka masa wuta saboda kasa samun aiki da shi da tayi
  • A bidiyon kai tsaye da tayi a TikTok, Bridget Thapwile Soko tayi rera waka tare da zunden wadanda suka kasa bata aikin bayan shekaru hudu da kammala digirinta
  • Sai dai kuma, Desmond Bikoko, shugaban jami’ar Exploit inda Bridget tayi karatu yayi hanzarin martani inda yace sun kwace digirinsu

Bridget Thapwile Soko, budurwa ‘yar kasar Malawi wacce tayi digiri a fannin kasuwanci ta fito bainar jama’a ta bankawa shaidar digirinta wuta.

Ta matukar fusata ne saboda shekaru hudu da ta kwashe da kammala karatu amma bata samu aiki ba.

Bridget
Bidiyon Budurwa da ta Kone Kwalin Digirinta Bayan Shekaru 4 Tana Neman Aiki. Hoto daga TikTok/ Bridget Thapwile Soko
Asali: UGC

A bidiyon kai tsaye da tayi a TikTok, matashiyar budurwar ta rera waka tare da zunden duk wanda ya gaza bata aiki ko kuma ya ki gayyatarta tantancewa.

Kara karanta wannan

Hotunan Diyar Jackie Chan Tana Rayuwa Cikin Fatara a Canada Sun Bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tace gara ta kone kwalinw digirin amma ta adana satifiket don aurenta. Muryoyi da aka ji a bidiyon sun tabbatar da cewa akwai mutane a tare da ita kuma sun yi mamaki.

Jami’ar Expoit tayi martani

Sai dai, makarantar da tayi ta gagauta yin martani bayan labarin abinda Bridget tayi ya kai mata.

Kamar yadda shugaban jami’ar Expoit, Desmond Bikoko ya bayyana, yace budurwar tayi hakan ne don zunde tare da zolayar jami’ar.

A wasikar da aka rubuta ranar 21 ga watan Oktoban 2021, makarantar ta kushe abinda budurwar tayi tare da kwace kwalin digirinta.

Wani bangare na wasikar yace:

“Cike da takaici muka gane cewa kin nadi bidiyon ko a digirin da muka baki bayan kin kammala karatu a jami’ar Expoit kuma kika wallafa a soshiyal midiya.
“A fassarar da muka yi, kin yi hakan ne don tozartawa tare da bata sunan jami’ar.

Kara karanta wannan

Ba a cire rai: Budurwa ta ba da mamaki, duk da faduwa a JAMB ta sau 7, ta kammata digiri

“A don haka jami’ar ta janye digirin da ta baki na fannin kasuwanci. Zamu bayyana hukuncin mu ga jama’a.
“Bayan haka, daga yanzu ke ba wacce ta kammala karatu bace daga jami’ar kuma digirin ki bashi da amfani.”

Wani Matashi Dan Shekara 21 Ya Mutu a Wurin Shagalin Bikin Karin Shekara

A wani labari na daban, Wani matashi ɗan shekara 21 a duniya, Micheal Arigbabuwo, ya rasa rayuwarsa a wurin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwa bayan haɗa manyan miyagun kwayoyi da suka sha ƙarfinsa.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng