Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

  • Majiyoyin tsaro sun tabbatar da rahotannin Amurka cewa akwai yan ta'addan Boko Haram a Abuja
  • Gwamnatin Amurka da ta Burtaniya sun gargadi 'ya'yansu mazauna Najeriya da su kula matuka kan yiwuwar samun hare-hare
  • Amma hukumar DSS tace yan Najeriya su kwantar da hankulansu babu abinda zai faru

Bayanai sun fara bayyana biyo bayan gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya sukayi cewa da yuwuwan yan Boko Haram sun kai hari birnin tarayya Abuja nan ba da dadewa ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun fara basaja da ayyukan hannu cikin birnin tarayya.

Rahoton yace wasu kwamandojin Boko Haram sun saje da jama'a kuma sun kammala shirin kai munanan hare-hare lokaci guda a Abuja.

Abuja
Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja
Asali: Twitter

Majiyoyi sun bayyana cewa yawancin ofishohin jakadancin kasashen waje dake Najeriya sun san da haka shiyasa suka sanar da yan kasashensu mazauna Najeriya cewa su yi hattara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP Ya Tunɓuke Wasu Hadimansa Daga Kan Mukamansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma hukumar DSS tace yan Najeriya su kwantar da hankulansu babu abinda zai faru

Wata majiya a hukumar tace

"Mun tsare birnin tarayya da kasar gaba daya... Yan ta'addan basu da wajen buya yanzu saboda muna bin diddiginsu muna kamasu."
"Duk mun san wayonsu. Da yawa cikinsu sun koma aiki kanikanci, tela, kafinta da lebura... mun san abinda ke faruwa."

Makarantun Boko Sun Tafi hutun dole

Legit ta tattauna da wata mammalakiyar makarantar 'Beauty of my deed' dake birnin tarayya Abuja kan halin da makarantu suka shiga.

Hajiya Jamila AbdulRahman ta laburta mana cewa wannan gargadi ya tilasta makarantu bada hutun mako daya na dole daga ranar Litnin kawo yanzu.

Tace:

"Nima jiya na samu labari makarantu sun rufe na tsawon mako guda, hakan ya sa na turawa iyaye sakonni kada su kawo yaransu makaranta."

Amurka da Burtaniya Sun Gargadi 'Ya'yansu Dake Najeriya Su Kula, Za a Iya Kai Hari Abuja

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya Sun Cafke Manyan Kwamandojin Boko Haram a Abuja da Kano

Gwamnatin Amurka da Burtaniya sun gargadi 'ya'yan kasashensu mazauna Najeriya da su kula, akwai yiwuwar samun hare-hare a Najeriya, musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na fitowa ne daga sashen ba da shawari kan tsaro na ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya

Ofishin ya kuma bayyana cewa, hare-haren ka iya aukuwa ne a gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni da shagunan siyayya, otal, mashawa, gidajen cin abinci da na wasanni har kan jami'an tsaro da sauransu.

A bangare guda, ofishin na Amurka ya ce, 'yan kasashen waje mazauna Najeriya da sauran kungiyoyin kasa da kasa ba za su tsira daga hare-haren ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida