Sojojin Najeriya Sun Cafke Manyan Kwamandojin Boko Haram a Abuja da Kano

Sojojin Najeriya Sun Cafke Manyan Kwamandojin Boko Haram a Abuja da Kano

  • Rahotanni sun bayyana yadda aka damke manyan kwamandojin Boko Haram a babban birnin tarayya na Abuja da jihar Kano a cikin kwanakin nan
  • An gano cewa, matsanta musu da jami’an tsaro suka yi a arewacin Najeriya yana daga cikin dalilan da suka da su tururuwar sauya wuraren zamansu
  • Sun dinga shirya makircin kaddamar da gagarumin harin da zai gigita Abuja da duniya baki daya domin nuna cewa suna nan da karfinsu, amma an dakile hakan

Kafin shawarar ranar Lahadi da ofishin jakadancin Amurka suka fitar da shawari, hukumomin tsaro suna ta aiki tukuru wurin gujewa farmaki a Abuja da kewaye na ‘yan ta’addan ISWAP, binciken Daily Trust ya bayyana.

Dakarun Soji
Sojojin Najeriya Sun Cafke Manyan Kwamandojin Boko Haram a Abuja da Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyin tsaro sun ce da yawan ‘yan ta’addan da masu taimaka musu suna ta kokarin shirya yadda zasu kaddamar da hare-hare da zai janyow hankali ne duniya, kuma an kama su a Abuja da yankuna masu makwabtaka.

Kara karanta wannan

Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

Majiyoyi we sun ce shawarar da ofishin jakadancin ya bayar gaskiya ce kan cewa ‘yan ta’addan na shirya tuggu ballantana a kewayen babban birnin tarayya.

Sun ce sun sauraron umarnin ne da shawara daga manyansu na ciki da wajen Najeriya kan yadda zasu kaddamar da harin a matsayin wata alama ta isa kuma su bayyana cewa suna nan da karfinsu sannan zasu iya kai hari ko ina.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gano cewa, suna ta tururuwar komawa Abuja ne sakamakon matsa musu lamba da rundunar sojin Najeriya tayi a arewacin Borno dake da iyaka da Chadi, Nijar da Kamaru da kuma dajikan Alagarno da dajin Sambisa a arewa masu gaba shine arewa.

Luguden wutan da ake yi wa ‘yan ta’addan a yankunan jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara sun a arewa maso yammacin Najeriya ya kawo ajalin mayakan masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

Rudani: Amurka da Burtaniya sun ce za kai hare-hare Abuja, sun ba 'ya'yansu dake Najeriya shawari

Wasu majiyoyi sun sanar da cewa wasu kwamandojin ISWAP da sojojinsu sun shige cikin jama’a a ciki da kewayen Abuja domin kaddamar da hare-harensu a lokaci daya.

Majiyoyin sun ce da yawa daga cikin ofis Osborn jakadanci dake kasar nan sun sani don haka sanarwar da ofishin jakadancin Amurka ya fitar yana daya daga cikin shawarin da ya dace a bai wa ‘yan kasa.

An kama manyan kwamandojin ‘yan ta’adda a Abuja

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, kusan makonni biyu da suka gabata ne aka kama wasu manyan ‘yan ta’adda a Tipper Garage da kuma kan babban titin Kubwa kusa da yankin Jahi.

A ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba, Abubakar Dan Borno, wani shugaban ISWAP da ya arce daga dajin Sambisa an kama shi a Mararaba, wani yankin Abuja a jihar Nasarawa bayan ya shiga hannu bayan kwanakin da aka kwashe ana bibiyarsa.

An mika wanda ake zargin hannun sojoji kuma an kai shi Cibiyar binciken sirri domin tuhuma.

Kara karanta wannan

Harin Babban Asibiti a Neja: 'Yan Bindiga Sun Aike Da Sakon Bukatunsu

Daily Trust ta bayyana cewa, bayanan sirri sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan dake harin Abuja suna rayuwa a Kaduna, Kano da sauran jihohin arewa maso yamma kuma suna zuwa Abuja lokaci bayan lokaci domin zantawa da sauran ‘yan ta’addan.

Majiyoyin sun ce wani Abubakar Musa wanda ke samarwa ISWAP kayan aiki an kama shi a sanar Litinin bayan bibiyarsa da aka dinga aka kama shi a kauyen Falgore dake karamar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano.

An gano cewa da yawansu an bibiye su kuma an kama su a matsayin hanyar tarwatsa mugun abunda suke shiryawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng