Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Da Sukayi Watsi Da Atiku Suka Koma Bayan Peter Obi
Ana saura kwanaki uku gudanar da zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Mayu, daya daga cikin manyan yan takaran Peter Obi, ya fita dgaa jam'iyyar.
Kai tsaye tshon gwamnan na Anambra ya koma jam'iyyar yan kwadago ta Labour Party kuma ya samu tikitin takara.
Tun bayan zama dan takarar kujerar shugaban kasa na LP, Obi ya samu shahara fiye da yadda ake tsammani.
Yanzu ana hasashen ma da yiwuwan Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasan.
Sakamakon haka, wasu jiga-jigan PDP sun yi watsi da Atiku da PDP sun koma bayan Peter Obi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta tattaro muku wasu daga cikinsu:
1. Dr Sampson Orji
Dr Sampson Orji, ya yi takaran kujerar gwamna karkashin PDP a jihar Abia amma yace shi fa Peter Obi zai zaba a 2023.
Orji kuma ya lashi takobin cewa ba zai fita daga PDP ba.
2. Babatunde Gbadamosi
Babatunde Gbadamosi, shahrarren dan siyasan adawa a jihar Legas ya yi takaran kujerar Sanata mai wkailtan Legas ta yamma.
Ya sauya sheka LP kum yana tare da Obi.
3. Chief Adesunbo Onitiri
Chief Adesunbo Onitiri, wani babban jigon jam'iyyar PDP ne a Legas kuma haka shima ya sauya sheka jam'iyyar LP.
4. Ogbeide Ifaluyi-Isibor
Ogbeide Ifaluyi-Isibor, jigo a PDP ya zama Diraktan tara jama'a na kamfen Peter Obi.
5. Cif Doyin Okupe
Dr Doyin Okupe, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Goodluck Jonathan tuni ya fita daga PDP.
Yanzu ya zama Dirakta Janar na kamfen Peter Obi na kasa
2023: Nan Ba Da Jimawa ba Yan Obidient Zasu Gaji, Ba Inda LP Zata Je, Obaseki
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kore duk wata damar samun nasara ga jam'iyyar Labour Party da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a babban zaɓen 2023.
Channels TV ta rahoto cewa Obaseki ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen jam'iyyar PDP na jiharsa ranar Litinin.
Gwamnan yace mabiyan Peter Obi waɗanda suka yi ƙaurin suna da "Obidients" nan ba da jimawa ba zasu rasa wannan tururin da zumudin da suke yi.
Asali: Legit.ng