Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

  • Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed, ya caccaki ‘dan takarar shugabancin kasa na LP, Peter Obi, kan bai wa dubban mutane tallafin biredi sunki 24
  • Ya kalubalanci tsohon Gwamnan jihar Anambran kan kyautar injin nika daya, kwalayen indomie, bargo da basu mai 100 ba ga dubban jama’a
  • Sai dai ba a kare lafiya ba a Twitter tunda mabiyan Obi sun dinga sukar hadimin shugaban kasan kan cewa babu abinda yayi na tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa dasu

Bashir Ahmad, mai bai wa shugaban kasan shawara kan sadarwa mai dogaro da fasahar zamani, ya zolayi Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar LP, kan tallafin da ya bai wa wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa dasu a jihar Anambra a baya-bayan nan.

Peter Obi
Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi. Hoto daga @peterobi
Asali: UGC

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, Obi ya bayyana wasu kayayyaki da ya bai wa mazauna yankin Ogbaru dake jihar Anambra da ‘yan gudun hijira a sansanin Atani.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

A abubuwan da suka bayyana a hotunan da ‘dan takarar ya wallafa akwai sunkin biredi, buhunan shinkafa, indomie, janareto da sauran kayayyaki.

“A Yau na ziyarci yankunan da suka samu ambaliyar ruwa kamar Ogbaru a jihar Anambra da sansanin Atani na ‘yan gudun hijira. A gaskiya an samu barna sosai ta ababen more rayuwa. Ina jajantawa jama’a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na yi alkawarin cewa masu duba mabukata zasu ziyarcesu tare da mika bayani ga gwamnatin tarayya da hukumomi don aikin farfado da yankin.
“A cigaban ziyarar da nake yi yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, na ziyarci Anambra ta gabas da yamma tare da masu ruwa da tsaki: Dr Tony Nwoye da Cif Peter Aniekwe. Gidaje sun nitse har rufinsu.
“Har yanzu ina mamakin dalilin da yasa gwamnatin tarayya bata ayyana ambaliyar ruwa matsayin dokar ta baci ba kuma ta fitar da yanayin kai dauki.”

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

- Tsohon Gwamnan yace.

A yayin martani, Ahmad a wallafar da yayi a Twitter a ranar Lahadi, ya zundi Obi kan kayan abinci ya baiwa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

“Tsohon Gwamna kuma ‘dan takarar shugabancin kasa yana bada tallafin injin markade da sunki 24 na biredi ga dubban jama’a da ambaliyar ruwa ta shafa. Kwamared, a 2022 muke don Allah. Muna kira gareka da ka mutunta iyalanka ka gyara.”

- Yace a Twitter.

Jama’a Sun Yi Masa Martani

Sai dai, jama’a sun dinga raddi ga hadimin shugaban kasar a Twitter kamar Haka:

@gechlife:

“Bashir mabiya 1.3 miliyan gareka. Da kayi amfani da wannan wurin ka taimaki miliyoyin ‘yan Najeriya da suka rasa gidajensu kuma suke bukatar abinci da sauransu. Sama da 600 sun mutu amma kana nan kana siyasa. Har yanzu kofofin a bude suke na karbar tallafi.”

@andyRoidO:

“Jaddada cewa tsohon gwamna ne ya nuna cewa Bashir na ganin gwamnati wani wurin sata ne. Abun mamaki, tunda yana cigaba da janye kudin gwamnati a matsayin albashi koda ya bar gwamnatin.”

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

@igweodyssey:

“Rashin kaifin kwakwalwa yana daga cikin abinda ake bukata na dole kafin zama mai goyon bayan Tinubu da APC kuma wallafar Bashir ta tabbatar da cewa Peter Obi ne abun tsoronsu.”

@Scizo4real:

“Nawa Buhari ya kai wa mutanen Daura? Kai ba komai bane baya da wawan yaro!”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng