Ina Cin Zabe A 2023 Zan Cire Tallafin Man Fetur, Farashi Zai Tashi: Tinubu

Ina Cin Zabe A 2023 Zan Cire Tallafin Man Fetur, Farashi Zai Tashi: Tinubu

  • Asiwaju Bola Tinubu ya hau mimbarin bayyanawa yan Najeriya manufofinsa idan ya samu cin zabe
  • Abu na farko Tinubu ya yi alkawarin cire tallafi man fetur da aka dade ana biya don saukin mai
  • NNPCL ta yi ikirarin cewa ana shan litan man fetur milyan 66 kulli yaumin a Najeriya

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin cire tallafin mai yana hawa mulki.

A takardar manufofinsa da ta yadu ranar Juma'a, Tinubu yace a cikin wata shida na farko zai aiwatar da sabuwar dokar PIA, zai cire tallafi kuma zai samar da wasu sabbin ka'idoji don janyo hankalin masu zuba jari.

A cewarsa:

"Zamu cire tallafin man fetur amma zamu samar da hanyoyin taimakawa mutane."

Kara karanta wannan

Jerin Bukatu 7 Da CAN Ta Gabatarwa Tinubu: Bukatu 2 Da Zai Yiwa Tinubu Wahalan Biya

"Zamuyi hakan ta zuba kudin tallafin wajen gine-gine, aikin noma, shirye-shiryen jin dadi wanda ya hada da gina titi, rijiyar burtsatsai, rage kudin mota, ilimi da kuma kiwon lafiya."
" Bayan cire tallafin mai, zamu mayar da hankali wajen gyara matatun man kasa tare da hada kai da wasu kasashe masu arzikin man fetur a fadin duniya."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu
Ina Cin Zabe A 2023 Zan Cire Tallafin Man Fetur, Farashi Zai Tashi: Tinubu
Asali: Twitter

Wai Shan Man Fetur Muke yi: Sanusi Lamido Yace Ta Yaya Ake Shan Litan Mai Milyan 66 a Rana

Zaku tuna cewa tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana rashin amincewarsa da ikirarin shan man fetur lita 66m a rana da NNPC tace anayi a Najeriya.

Sanusi ya bayyana cewa ta yaya za'a rika shan wannan adadin man fetur kulli yaumin tun da ba ruwan sha bane.

Kara karanta wannan

Gidana Ni Kadai Ne Musulmi, Dukkan Iyalina Kiristoci ne: Tinubu Ya Laburtawa CAN

Tsohon Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Asabar a taron zuba jarin jihar Kaduna KadInvest7.0, rahoton ChannelsTV.

Yace:

"Wai shina shan man fetur muke yi kamar ruwa?"
"NNPC na fada mana cewa mun shan litan mai milyan 66 a rana. Muna sha fiye da Indonesia, Pakistan, Egypt, Cote d’Ivoire, da Kenya."
"A 2019, litan mai milyan 40 muke shigowa da shi. Yanzu a 2022, lita milyan 66. Cikin shekaru uku, mun kara yawan shan mai da kashi 50%. Shin adadinmu ne ya kara yawa? motoci ne suka kara yawa? Ka tambayi kan ka, ta yaya hankali zai dauki wannan."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida