Gwamnati Ta Fadawa MTN, Glo, Airtel Su Dakatar da Karin Farashin Da Suka Yi a Boye

Gwamnati Ta Fadawa MTN, Glo, Airtel Su Dakatar da Karin Farashin Da Suka Yi a Boye

  • Hukumar kula da harkokin sadarwa ta bukaci a dakatar da karin kudin waya da hawa yanar gizo
  • A watan Oktoban nan aka fahimci kamfanonin sadarwa sun canza farashin yin waya da sayen ‘Data’
  • NCC tace kamfanonin sun dauki wannan mataki ne su kadai, bayan an bukaci a janye batun karin 10%

Abuja - Hukumar da ke sa ido wajen harkar sadarwa a Najeriya ta NCC, ta fadawa kamfanonin da ke aiki a kasar su dakatar da karin farashin da suka yi.

A watan da ya gabata kamfanonin sadarwa su ka kara kudin yin waya da farashin sayen ‘data’ na hawa shafukan yanar gizo, la’akari da wasu abubuwa.

Jaridar This Day a rahoton da ta fitar a ranar Alhamis, tace kamfanonin sun dauki wannan mataki ne suka kadai bayan an amince farashi su karu da 10%.

Kara karanta wannan

An Samu Tashin Hankali A Shahhararriyar Kasuwar 'Alaba International', Mutane Da Dama Sun Jikkata

Darektan yada labarai na Hukumar NCC, Reuben Muoka ya fitar da jawabi a Abuja, yana bayanin yadda da farko aka amince da karin 10% a farashin waya.

Reuben Muoka yake cewa an amince da karin kudin ne kamar yadda dokar NCC ta shekarar 2003 ta amince, duba da yadda ake gudanar da kasuwanci a yau.

Premium Times tace a Satumban da ya wuce aka dakatar da karin farashin da aka yi niyya bayan korafin jama’a, sai kwatsam aka ga farashi ya canza yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NCC tace kamfanonin sun yi wannan karin farashi ne ba tare da sun bada sanarwa ba. Hakan na zuwa ne bayan gwanati ta dakatar da yin karin.

Muoka yace duk da abubuwa sun yi tsada, kamfanonin sadarwa suna cin riba a haka, don haka babu dalilin a kara farashi ta yadda al'umma za su sha wahala.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8

Shugaban NCC
Shugaban NCC da Ministan sadarwa Hoto: techeconomy.ng
Asali: UGC

Irin canjin da aka samu

Misali farashin 2.5GB na ‘Data’ da ake saye a kamfanin MTN ya tashi daga N500 zuwa N550. Legit.ng Hausa ta fahimci irinsu Airtel na 2GB ya karu da 10%.

Haka zalika tsarin Airtel 40GB da mutane suka saba saye a kan N5000 a baya, ya karu zuwa N5500. Babu ranar da kamfanoni suka bada sanarwar canjin.

Daga N1100, abin da Airtel take saida 1.5GB ya dawo N1200, haka lamarin yake a sauran farashin ‘Data’ na 3GB, 4.5GB, 6GB, 10GB, 11GB da kuma 20GB.

Kamfanin MTN ya canza kudin sayen ‘Data’ na wata-wata. 1.5GB, 2GB, 3GB, 4.5GB da 6GB sun dawo N1100, N1200, N1500, N2000 da N3500 a halin yanzu.

Minista ya sa a hana kara farashi

Kwanakin an ji labari Ministar sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya sa baki an hana kara farashin waya da hawa yanar gizo.

Kara karanta wannan

EFCC: ‘Dan Damfara Ya Rasa Dukiyarsa Har Abada, Ya Sallama Kudi, Bitcoin na N40m

Ministan ya aikawa shugaban kasa wasuka, yana mai yi masa kukan cewa tsadar amfani da wayoyin salula da yanar gizo yana da illa ga tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng