Dino Melaye Ya Saki Bidiyon Karyata Cewa Atiku Jinya Ya Tafi Faransa
- Sanata Melaye ya saki bidiyon dan takaran shugaban kasa na jam'iyyar PDP yana jin dadinsa a kasar Faransa
- Jam'iyyar APC a jiya tace an garzaya da Atiku kasar Faransa don ganin Likita sakamakon suma da yayi
- Bidiyo ya nuna Melaye yana jawabin cewa ga Atiku nan cikin koshin lafiya amma ance bai da lafiya
Daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dino Melaye, ya saki sabon bidiyon maigidansa, Atiku Abubakar.
Melaye ya sakin bidiyon kansa da dan takarar kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar; hadiminsa Timi Frank, Daniel Bwala da Ndudi Elumelu.
Ya saki bidiyon ne matsayin martani ga ikirarin jam'iyyar APC cewa jinya suka kai Atiku kasar waje.
A faifain bidiyon, Melaye yace:
"Ku kalli wanda aka ce yana asibiti. Shin nan ya yi kama da asibiti? Gashi yana cin abinci, yana hutawa, yana jin dadin kansa, yana ganawa d amutane. Allah ya raba mu da yunwa, yunwa ba tada hankali."
Kalli bidiyon:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Femi Fani-Kayode ya fito yana cewa Atiku Abubakar ya kamu da rashin lafiya ana tsakiyar yakin takara
Tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode ya yi ikirari Atiku Abubakar mai nemam zama shugaban kasa a jam’iyyar PDP bai da lafiya.
Ana zargin an fita da ‘dan takarar shugabancin kasar na 2023 zuwa ketare domin ya ga Likita, amma hadimin Atiku Abubakar ya musanya hakan.
Cif Femi Fani-Kayode wanda yanzu shi ne Darektan yada labarai a kafar zamani na kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu ya bayyana haka.
A wani bayani da ya yi a shafin Facebook a yammacin Talata, Femi Fani-Kayode yace Atiku Abubakar ya fara rashin lafiya bayan barin Kaduna.
Jawabin Femi Fani-Kayode
"Bayan yawon kamfe da ya yi jiya a Kaduna, Atiku Abubakar ya kamu da mummunan rashin lafiya.
Ya koka da cewa yana jin jiri da matsanancin zafi a kai da kuma duka jikinsa a cikin jirgin sama a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.
Bayan ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Abuja, sai ya fadi. Nan take aka wuce da shi zuwa birnin Faris (Faransa).
Asali: Legit.ng