Matar Aure Ta Bayyana Yadda Kidinafas Suka Bata N2,000 Bayan Karbar N6m daga Mijinta
- Hajiya Fatima Ibrahim ta bayyanawa alkali yadda masu garkuwa da mutane suka bata N2,000 daga cikin N6 miliyan na kudin fansa da mijinta ya biya
- Ta sanar da yadda masu garkuwa da mutanen suka sace ta a Zaria sannan bayan karbar kudin fansa suka yi mata kwatancen inda zata samu motar zuwa gida
- Sun fara kai ta dajin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna bayan sun so sace mijinta amma basu same shi a gida ba
Zaria, Kaduna - Wata shaidar masu gurfanar mai suna Hajiya Fatima Ibrahim ta sanar da wata babbar kotu dake zama a Zaria cewa wadanda suka yi garkuwa da ita sun baya N2,000 kudin mota bayan sun amsa N6 miliyan na fansa.
‘Yan sanda sun gurfanar da Dalhatu Shehu, Lawal Aliyu Bullet, Nuhu Ismaila da Nura Usman kan hada kai wurin aikata laifi, fashi da makami, mallakar makamai ba bisa kaida ba da garkuwa da mutane.
Laifukan kamar yadda ‘yan sandan suka ce sun ci karo da tanadin sashi na 59, sakin layi na 1, sashi na 246 na Penal Code da sashi na 6 na dokokin mallakar makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta rahoto cewa, Ibrahim tana bada shaida ne a zaman kotun da aka yi a Dogarawa dake Zaria.
“A ranar 2 ga watan Janairun 2021 da dare na ji wasu irin hayaniya a gidana. A yayin da na tashi daga bacci da ma kunna wuta. Na ga mutum hudun nan da ake tuhuma da wuka da adda.
“Suna son sanin inda mijina yake amma na sanar musu baya gari.
“Sun yi garkuwa da ni kuma sun kai ni dajin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna bayan sun kwashe kudi, kayan yara da sauran abubuwa masu amfani daga gidana.
“Sun kira mijina kuma sun yi yarjejeniyar cewa zai biya kudin fansa N6 miliyan kuma a biya biyu.
“A gabana aka biya kudin kuma mutum na hudu da aka gurfanar mai suna Usman ya bani N2,000 daga ciki don in yi kudin mota.”
- Ta sanar da kotun.
Tace wadanda aka gurfanar din sun yi mata kwatancen inda zata samu abun hawa da zai kai ta gida kuma sun tabbatar mata babu wani abunda zai faru da ita da sauran.
Bayan lauyan wadanda ake kara A Y Musa ya kammala ji, lauyan ya tambaya Ibrahim wanda ya kai kudin fansan ga wadanda ake zargi.
“Ban san sunansa ba amma na san shi saboda tana aiki da mijina.”
- Tace.
Lauyan masu gurfanarwan, Jummai Dan Azumi ta bukaci da a sallami shaidar.
Mai shari’a Kabir Dabo ya sallami shaidar inda ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba.
Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Samo Kudin Fansa N8.4m a Bauchi
A wani labari na daban, wasu da ake zargi da zama masu garkuwa da mutane har su biyu sun sheka lahira sakamakon musayar wuta ne da suka yi da jami’an ‘yan sanda a kauyen Maina-Maji dake karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Har ila yau, ‘yan sandan sun damke wani matashi mai shekaru 20 mai suna Abubakar Isah da zargin garkuwa da mutane dauke da N8.4m da ake zargin kudin fansa ne ya karba daga jama’a.
Asali: Legit.ng