Da Duminsa: Gwamnati Ta Tanadi N470bn Don Karawa Malaman Jami'a Albashi Da Gyara Jami'a
- Ministar Kudin Najeriya ta bayanin tanadin na musamman da gwamnati ta yiwa Malaman ASUU
- Hajiya Zainab tace wannan kari zai bayyana na a kasafin kudin 2023 da Buhari ya kai majalisa
- Kungiyar Malaman jami'a ta janye daga yajin aikinta bayan watanni takwas ana gwagwarmaya
Abuja - Gwamnatin tarayya ta tanadi karin kudi na musamman na N470bn a kasafin kudin 2023 don karin albashin malaman jami'o'in Najeriya da kudin gyara jami'o'in.
Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ranar Laraba yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, rahoton ChannelsTV.
Ta ce musamman aka yi wannan karin don Malaman jami'an da suka kammala yajin aiki makon da ya gabata.
Tace za'a yi karin albashi da N170bn sannan a gyara jami'o'in da N300bn.
A cewarta, har yanzu gwamnati ta shan wahalar samun kudin shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Game da wasu rassa kuwa, tace an tanadi 2.05 trillion don sashen Ilimi yayinda aka tanadi 1.58tr don kiwon lafiya.
Hakazalika aka ware 2.74tr don tsaro sannan aka tanadi 998.9 billion don manyan gine-gine, sannan 756 billion don rage talauci.
Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU
Shugaban kungiyar ASUU ta malaman jami’a, Emmanuel Osodeke yace hukuncin kotu ne babban abin da ya tursasa masu komawa bakin aiki.
The Cable ta rahoto Farfesa Emmanuel Osodeke yana mai cewa malamai sun janye yajin-aikin da su ke yi ne saboda Alkali ya umarci su bude makarantu.
Kungiyar ASUU tace duk da an janye yajin-aikin bayan watanni takwas, har yanzu ba ta cin ma matsaya da gwamnatin tarayya kan wasu batutuwan ba.
Da aka zanta da shi a gidan talabijin na Channels, Farfesan yace kungiyarsu tana sa ran gwamnati za tayi abin da ya dace tun da sun dawo bakin aikinsu.
A hirar da aka yi da shi, Osodeke yace duk da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya sa baki a lamarin, kotu tayi tasiri wajen daukar matsaya.
Ba a gama shawo kan matsalolin ba, kuma babu wata yarjejeniya da aka cin ma. Saboda mun dawo aiki ne saboda mu kungiya ce mai bin doka.
Ba mu son yi wani abin da zai saba doka. Muna sa ran sa-bakin da shugaban majalisa ya yi, kamar yadda ya yi alkawari zai kawo mafita da wuri."
- Farfesa Emmanuel Osodeke
Asali: Legit.ng