‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8
- Tsagerun 'yan bindiga sun kai hari Hayin Banki da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara
- Maharan sun yi awon gaba da mutane tara inda suka kashe daya daga cikinsu
- Rundunar yan sandan Zamfara ta tabbatar da faruwar al'amarin inda tace tana kokarin ceto mutanen
Zamfara - 'Yan bindiga dauke da makami sun farmakin garin Hayin Banki da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara a daren ranar Litnin inda suka kashe mutum daya da kuma awon gaba da wasu takwas.
Majiyoyi daga hedkwatar karamar hukumar sun sanar da Channels TV cewa yan bindigar sun mamayi yankin ne da misalin karfe 11:30 na dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi.
Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin mutanen da aka sace sun kasance ma’aikatan wani kamfanin ruwa da wani manajan gonar kaji.
Majiyar ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yan bindigar sun shiga Anka a daren jiya, ta yankin Hayin Banki sannan suka sace mutum tara amma an tsinci gawar daya daga cikin mutanen. Sun kuma sace dabbobi da dama.”
Yankin karamar hukumar Anka na ta fama da hare-hare da dama tun a farkon shekarar nan kuma yana daya daga cikin kananan hukumomin da gwamnatin jihar ta rufe kwanan nan.
Kakakin yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ce rundunar ta tura jami’ai zuwa yankin sannan ana kokarin ceto mutanen.
Ya ce:
“Da gaske ne, muna kan lamarin, rundunar ta tura jami’ai zuwa yankin da nufin ceto mutanen cikin koshin lafiya.”
Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Rufe Gidajen Talabijin da Rediyo Saboda Rashin Da'a
A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta rufe gidajen talabijin uku da gidan radiyo daya a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, saboda saba ka'idar aikinsu.
Gidajen talabijin da abun shafa sun hada da NTA, Gamji TV, Al-umma TV da Pride FM dukkansu a Gusau, babban birnin jihar, jaridar Punch ta rahoto.
A wani jawabin radiyo, kwamishinan labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ce an rufe gidajen labaran ne saboda sun keta ka'idar aikinsu.
Asali: Legit.ng