Kyari: NDLEA Bata da Hurumin Gurfanar dani, Ina Rokon Kotu Tayi Watsi da Kararta
- Dakataccen shugaban rundunar IRT, DCP Abba Kyari ya mika bukatar kotu tayi watsi da laifukan da NDLEA ke tuhumarsa da su baki daya
- A cewar kwararren ‘Dan sandan, NDLEA basu da hurumin tuhumarsa tunda kwamitin ladabtarwa ta hukumar ‘yan sanda bata titsiye shi ta tuhume shi ba
- Sai dai wata majiya tace DCP Abba Kyari baya son wasu Umeibe da Ezenwanne su bada shaida kansa kan harkallar miyagun kwayoyin da ake zarginsa da ita
FCT, Abuja - A kokarin dakatar da gurfanarsa a gaban kotu kan zargin safarar miyagun kwayoyi, dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, ya mika bukata a gaban kotu kan tayi watsi da zargin laifukan da Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA take masa.
Tsohon kwamandan rundunar IRT sun yayi ikirarin cewa bai dace a cigaba da zaman kotun ba saboda ba a gurfanar da shi a kwamitin ladabtarwa ba hukumar ‘yan sandan Najeriya ba kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.
Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kyari, DCP Sunday Ubuha, ASP Bawa James da Sifetoci Simon Agirigba da John Nuhu a halin yanzu ana shari’arsu kan zargin laifuka biyar na safarar miyagun kwayoyi.
Bukatar da aka mika tana dauke da kwanan wata 12 ga Oktoban 2022 an shigar da Ita ne a ranar Alhamis da ta gabata ta hannun tawagar lauyoyin Kyari karkashin jagorancin Dr Ikpeazu Ikpeazu, SAN.
Wannan na zuwa ne kafin shiga kotun Kyari da mukarrabansa da za a yi a ranakun Laraba, Alhamis da Juma’a a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake Abuja.
Jaridar Punch ta tattaro cewa an mika wannan bukatar ne domin hana shaidun masu gurfanar Chibuna Umeibe da Emeka Ezenwanne bada shaidarsu kan zarginsa da ake ti da safarar miyagun kwayoyi.
Umeibe da Ezenwanne wadanda an taba kama su da laifukan harkallar miyagun kwayoyi zasu bada shaida kan Kyari, Ubuha, James, Agirigba da Nuhu a yayin da za a yi zaman kotun a ranar Laraba.
Jaridar Punch ta gano cewa, Hukumar NDLEA zata soki bukatar wacce aka saka ranar Laraba domin saurarenta.
Tun farko Kyari ya mika bukatar belinsa wanda kotun ta ki amincewa da ita saboda rashin isassun takardu da shaidu.
Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba
A wani labari na daban, rahotanni daga wata babbar kotun tarayya da ke Abuja sun ce, kotun ta ki bayar da belin DCP Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar (DCP) bisa wasu tuhume-tuhume.
The Cable ta ruwaito cewa, mai shari'a Inyang Ekwo, ya yanke hukunci a ranar Litinin, cewa bukatun da aka bijiro dasu sun wuce gona da iri.
Asali: Legit.ng