Ke Tauraruwa Ce: Makauniyar ‘Yar Najeriya Ta Doke ‘Yan Mata 18, Ta Ci Gasar Kyau a Bidiyo
- Wata budurwa mai lalurar makanta ta lallasa tsala-tsalan yan mata 18 wajen lashe gasar sarauniyar kyau na birnin Port Harcourt na 2022
- Favour Rufus bata gani kwata-kwata a ido daya sannan bata gani sosai da dayan idon kuma tana bukatar magani
- Sai dai nasararta a gasar ya baiwa mutane mamaki domin hakan ya zama madubin dubawa ga wasu da dama
Rivers - Favour Rufus, budurwa wacce ta hadu da lalurar makanta tun tana da shekaru 18 a duniya, ta lashe gasar sarauniyar kyau na 2022 da aka yi a birnin Port Harcourt.
A wata hira da sashin BBC Pidgin, Favour ta bayyana cewa idonta na hagu a makance yake kuma tana bukatar ganin likita akai-akai don amfani da daya idon.
Ta kuma ce daya idon nata zai makance idan ta yi kuskure wajen magani. Duk da haka, makantanta bai hana ta ci gaba a rayuwa ba.
Yadda Favour ta makance
A wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, Favour ta ce ta fara samun matsala da idonta ne tana da shekaru 6.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ta kai shekaru 8, likitoci sun tabbatar da cewa ta rasa idonta na hagu gaba daya kuma cewa tana bukatar ganin likita akai-akai don amfani da daya idon.
Yadda Favour ta lashe gasar sarauniyar kyau na Port Harcourt
Favour tace ta shiga gasar ne da don ta ji a jikinta zata iya duk da cewar wasu da dama sun sanyaya mata gwiwa.
Ta yi takara da wasu mata 18, amma itace ta yi nasara. Ta bayyana a bidiyon tare da mahaifiyarta wacce ta bayyana a matsayin bangon jinginarta.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin jama'a
Anastecia Cyril ta ce:
“Wow na tayaki murna yar’uwa. Wannan abu akwai burgewa a ciki sosai. Allah buwayi gagara misali ya dawo maki da ganinkin Ameen.
Tamunoene Victor-mark:
“Ina tayaki murna mai kyau. Ke tauraruwa ce kuma rahama ce. Allah madaukakin sarki ya ci gaba da kareki don cika burinki,. Ameen.”
Kara Tsawo Nake Duk Bayan Wata 3 Ko 4: Wani Dogon Mutum Ya Ba Da Tarihinsa A Wani Bidiyo
A wani labarin, wani mutumi mai suna Sulemana Abdul Samed wanda aka fi sani da Awuche da ake yiwa kallon mutum mafi tsawo a kasar Ghana ya bayyana cewa yana kara tsawo duk bayan watanni uku ko hudu.
Abdul ya yi fice a duniyar yanar gizo kuma ya zama shahararre a garinsa saboda yanayin halitarsa ta dogon mutum.
A wata hira da BBC News Pidgin, mutumin yace ya fara lura da ya fara tsawo ne a cikin shekarar 2015.
Asali: Legit.ng