Yadda Wata Mata Ta Ɗana Wa Malaman Ɗanta Tarko Ta Gano Su Ke Cinye Masa Abinci A Makaranta

Yadda Wata Mata Ta Ɗana Wa Malaman Ɗanta Tarko Ta Gano Su Ke Cinye Masa Abinci A Makaranta

  • Wata mata ta yi mamakin yadda kowane rana danta zai dawo gida daga makaranta ba tare da ya rago abinci ba
  • Domin tabbatar da abin da ta ke zargi, ta tura yaronta makaranta da abincin da ta san baya kauna amma ya dawo an cinye baki daya
  • Matar ta ce daga nan ne ta tabbatar da abin da ta ke zargi na cewa malamansa ne suka cinye abincin da ta ke bashi

Twitter - Wata mahaifiya wani yaro a Najeriya mai suna @Dcounty93 a Twitter ta zargi malaman makarantar yaronta suna cinye masa abinci.

Matar ta ce ta dade tana zargin wani na cinye abincin dan ta mai shekara biyu wanda a kullum ta ke saka masa abinci a kwano ya tafi da shi makaranta.

Dan makaranta, mahaifiyarsa da abinci
Yadda Wata Mata Ta Dana Wa Malaman Danta Tarko Saboda Cinye Masa Abinci, Ta Ce Baya Cin Abinci Da Yawa A Gida. Hoto: @Bassey Edoho / Jasmin Merdan.
Asali: Getty Images

Duba da cewa ta san danta baya son danyen plantain, ta saka masa a cikin kwano ta tura shi makaranta. Abin mamaki, ya dawo gida kwanon babu komai.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Gwamnan PDP ya nada masu bashi shawara kan harkar siyasa mutum 50,000

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalamanta:

"Na saka masa dafaffen danyen plantain da kwai/miyan alayyaho! Na san tabbas da na baya son danyen plantain. Ai ko sai da dawo da kwano babu komai.
"Dama gwaji ne, saboda kwanonsa yana da girma kuma dan shekara biyu ba zai iya cinye abincin da ke ciki tashi guda ba. Na san akwai matsala! Ya kamata ya rago kadan ya dawo da shi gida. Dole na yi gwajin na ranar! Amma na samu amsa na. Lokacin ne na san malamansa na cin abinci sosai!."

Mutane sun yi martani yayin da mahaifiya ta zargi malaman makaranta da cin abincin dan ta

Ifunanya 13 ta ce:

"Me yasa za ki bashi abin da kin san ta yi wu ba zai ci ba? Kamar ranar ba ki son kwanciyar hankali."

Ife ta ce:

"Idan da malaman sun sani."

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

Mimeee Makas ta rubuta:

"Ni ma na dade ina mamakin yadda da na ke cinye abinci a makaranta kullum amma baya nauyi ya shigo gida."

Prince Lyf ya kara:

"Makaranta da damuwa ai. Wahalar = Malami."

Ga sakon a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164