Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

  • Kungiyar malamai masu koyarwa ta Jami’o’i a Najeriya ta bayyana janye yajin aikinta a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoban 2022
  • Sai dai Farfesa Osodeke ya bayyana cewa ba a Magance matsalolin da suka sa suka je yajin aikin ba har a halin yanzu
  • Osodeke ya bayyana cewa, su masu biyayya ne ga umarnin kotu kuma sun duba rokon Buhari da kokarin Gbajabiamila

FCT, Abuja - Kungiyar Malamai ta Jami’o’i ASUU ta janye yajin aikinta da ta kwashe tsawon wata takwas tana yi.

Sai dai a takardar da kungiyar ta fitar kuma jaridar Punch ta gani, tace har yanzu da suna cikin rikici da gwamnatin tarayyya kuma ba a shawo kan bukatunsu ba.

Farfesa Osodeke
Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba. Hoto daga TheCable
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da Duminsa: APC ta Aikewa INEC Wasika, Ta Bukaci a Karba Machina ‘Dan Takarar Sanata

Takardar da aka saki ga manema labarai wacce ta samu da hannun shugaban kungiya, Farfesa Emmanuel Osodeke, ta yabawa ruwa da tsakin da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yayi wirin shawo kan matsalar.

Wani sashi na takardar yace:

“Hukumar zartarwa ta kasa ta zasu tayi taron gaggawa a sakateriyarta ta kasa dake Jami’ar Abuja a ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoban 2022.”

A takardar da kungiyar ta fitar ta kara da bayyana cewa Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige ya maka malaman a kotu.

“A fasahar kotun masana’antu ta kasa, ta baiwa ASUU umarnin komawa aiki kafin a kammala shari’ar. Bayar da irin wannan umarnin kuma tare da ra’ayin lauyan, an daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.
“A ilimin kotun daukaka karar kan abinda kungiyar ke bukata, ta sake jaddada umarnin kotun kasa a matsayin sharadin da zai sa ta saurari daukaka karar.
“NEC ta kiyaye dukkan tarukan da aka yi da shugabannin majalisar wakilai karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila tare da sa bakin manyan ‘yan Najeriya a ciki da wajen gwamnati.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU ta Janye Yajin Aiki

A yayin cigaba da magana kan matsayar yarjejeniyarsu, kungiyar tace:

“Yayin da muke yabawa da kokarin majalisar wakilai da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa da suka shiga lamarin, NEC na takaicin sanar da cewa har yanzu ba a shawo kan matsalar ba yadda ya dace.
“Sai dai a matsayin kungiyar na mai bin doka da rokon da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi tare da kokarin Femi Gbajabiamila da sauran ‘yan Najeriya, NEC din ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.
“Don haka dukkan mambobin ASUU ana umartarsu da su koma bakin aiki daga karfe 12:01 na ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba.”

Da Duminsa: Kungiyar Malama Jami’o’i, ASUU ta Janye Yajin Aiki

A wani labari na daban, kungiyar Malamai Masu Koyarwa ta Jami’o’i, ASUU, ta janye yajin aikin wata takwas da ta kwashe tana yi amma cike da sharudda.

Kamar yadda rahotannin da suka riski jaridar Vanguard suka bayyana, kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan ganawa da shugabanninta a daren Alhamis wanda har suka kai sa’o’i farko na ranar Juma’a suna tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng