Da Duminsa: Kungiyar Malama Jami’o’i, ASUU ta Janye Yajin Aiki
- Kungiyar Malamai Masu Koyarwa ta Jami’o’i, ASUU, sun janye yajin aikin da suka kwashe wata takwas suna yi amma a kan sharadi
- Kungiyar ta zauna taro da shugabanninta a sakateriyarta dake Abuja bayan an kammala na rassanta a ranar Laraba
- Kamar yadda aka sani, kotun daukaka kara ce ta umarci malaman makarantar da su koma aji kafin a cigaba da sauraron shari’arsu
Kungiyar Malamai Masu Koyarwa ta Jami’o’i, ASUU, ta janye yajin aikin wata takwas da ta kwashe tana yi amma cike da sharudda.
Kamar yadda rahotannin da suka riski jaridar Vanguard suka bayyana, kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan ganawa da shugabanninta a daren Alhamis wanda har suka kai sa’o’i farko na ranar Juma’a suna tattaunawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kira taron ne domin tantance matakin dauka bayan rassansu sun yi taro kan hukuncin kotun daukaka kara a makon jiya.
Kotun daukaka karar ta umarci ASUU da ta janye yajin aikinta kafin a saurari shari’arsu ta daukaka karar da suka yi.
Mambobin kwamitin zartarwa na kasa wadanda suka hada da shugabannin rassan su da shugabanninsu na kasa sun halarci taron ASUU da aka yi a sakateriyarsu ta kasa dake Abuja.
Idan za a tuna, kungiyar ASUU ta fada yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, watanni takwas kenan cif.
Gwamnati Za Ta Baiwa Malaman ASUU N50bn Kudin Alawus, N170bn Kudin Karin Albashi
A wani labari na daban, Punch ta ruwaito cewa za'a mayar da ragamar biyan kudin alawus na ma'aikatan jami'o'in Najeriya hannun majalisar jagorancin jami'o'in gwamnatin tarayya daga 2024.
Hakazalika gwamnati za ta saki kudi naira bilyan hamsin (N50bn) don biyan kudin bashi na alawus da Malaman ke bi kafin lokacin.
Wata majiya cikin majalisar zartaswar ASUU ta bayyana hakan ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.
A cewar majiyar:
"Game da lamarin alawus, an tanadi Bilyan 50 don biyan bashin da muke bi yayinda aka tanadi N170bn na karin albashi."
“Amma daga 2024, majalisar jagorancin jami'o'i ne zasu rika biyan alawus yayinda za'a zuba N300 billion wajen gyara makarantu."
Asali: Legit.ng