Matashi Mara Kafafu da Hannaye Yana Sarrafa TikTok a Bidiyo da Lebensa, Ya Ba Jama’a Mamaki
- Wani mutum mai nakasa mai suna Gabe Adams-Wheatley ya kwatanta wani abun mamaki na yadda yake amfani da lebensa
- Gabe wanda aka haifa babu kafafu balle hannaye yana amfani da TikTok da lebensa na sama kuma cike da hanzari
- Mutumin ya nuna kwazonsa a wani bidiyo wanda ya matukar birge ‘yan soshiyal midiya yayin da wasu kuwa saurinsa ya dauki hankalinsu
Gabe Adams-Wheatley wani mutum ne mai nakasa wanda ya bai wa jama’a mamaki da yadda yake amfani da labbansa.
Ya bayyana yadda yake amfani da labbansa a shafinsa na TikTok domin martani ga jama’a da suke tunanin ba zai iya martani kan tsokacinsu ba na soshiyal midiya saboda rashin hannayensa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yayin amfani da lebensa na sama cike da sauri, Gabe ya bude manhajar tare da yin tsokaci ba tare da taimakon kowa ba.
A yayin martani ga tsokacin da aka yi a kasan bidiyon, ya bayyana yadda fuskar wayarsa take bayan yayi amfani da lebensa wurin budeta.
‘Yan soshiyal midiya sun yi martani
Phea Plumlee391 tace:
“Ina alfahari da kai, wannan abu yayi kyau.”
Case Duarte yace:
“Wannan abu da birgewa yake! Ya idanunka suke? Da kyar nake iya rubutu da kumbuna na.”
Allana S tace:
“A gaskiya kana da sauri, kana rubutu da sauri fiye da ni kuma ina da yatsu.”
Tegan Vincent-Cooke yace:
“A gaskiya wannan abun birgewa ne.”
BillyBob tace:
“Idan fa mutum ya dauke ka tare da arcewa.”
Bayan Shekaru 47 da Barin Gida Yana Matashi, Ya Dawo a Tsoho, Babu Arzikin da Yaje Nema
A wani labari na daban, Bidiyon tsohon da ya dawo gida daga kasar waje bayan kwashe shekaru 47 ya bai wa jama’a mamaki.
A bidiyon, mutumin ya tsufa kuma kwatsam ya tuna gida tare da dawowa inda ya bai wa ahalinsa mamaki.
Labarin mutumin mai suna Peter Shitanda an wallafa shi ne a YouTube a tashar Afrimax ta Turanci kuma ta janyo cece-kuce.
Peter ‘dan asalin kasar Kenya ne kuma ya bar kauyensu inda ya koma kasar Tanzania tare da fatan zai yi arziki mai yawa.
Ya fara zama a Nairobi kafin ya koma Tanzania inda yayi aiki kusa da tsaunin Kilimanjaro.
Asali: Legit.ng