Wani Mutumi Dan Shekara 51 Ya Lakada Wa Matarsa Dukan Tsiya Har Lahira a Ogun
- Wani mutumi ɗan shekara 51 a duniya ya shiga hannu bisa tuhumar kashe matarsa kan karamin sabani a jihar Ogun
- Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, yace ƙanwar matar ce ta kai rahoton abinda ya faru ga yan sanda
- Kwamishinan yan sandan Ogun ya ba da umarnin maida Kes ɗin sashin aikata manyan laifuka domin tsananta bincike
Ogun - 'Yan sanda sun kama wani Magidanci ɗan shekara 51, Oluranti Badejo, bisa zargin dukan matarsa yar shekara 40, Folasade Badejo, har rai ya yi halinsa a jihar Ogun.
Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa lamarin ya auku ne a yankin Orimerunmu da ke ƙauyen Mowe, ƙaramar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a ranar Alhamis, yace wanda ake zargin ya shiga hannu bayan ƙanwar matar ta shigar ƙorafi a Caji Ofis ɗin Mowe.
A cewarsa, ƙanwar matar da aka ƙashe ta gaya wa yan sanda cewa an gaya mata Mijin ne ya lakaɗa mata dukan kawo wuƙa har ta mutu kan wani karamin saɓani.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wane mataki yan sanda suka ɗauka bayan samun rahoto?
Oyeyemi ya ƙara da cewa DPO na caji Ofis ɗin Mowe, SP Folake Afeniforo, bayan samun rahoton nan take ya tura dakaru wurin inda suka damƙe wanda ake zargi.
Kakakin 'yan sanda yace:
"Gawar Mamaciyar na kwance a wurin daga nan aka ɗauke ta zuwa ɗakin aje gawarwaki a Sagamu domin yi mata gwaji. Binciken farko ya nuna cewa mutumin ya shaƙe matar lokacin da suka fara faɗa kan ɗan karamin saɓani."
"Da ya fahimci ta mutu, wanda ake zargi ya yi amfani da Dutsen Guga na wuta ya kona wasu sassan jikin gawar matar domin ya koma tamkar Lantarki ce ta yi ajalinta."
"Amma bisa sa'a ɗiyarsa yar shekara 8 na wurin kuma komai a kan idonta ya auku. Yarinyar ce ta shaida ganin mahaifinta lokacin da ya shake mahaifiyarta."
Kwamishinan yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya umarci a maida Kes din ɓangaren kisan kai na sashin binciken aikata manyan laifuka domin tsananta bincike, Leadership ta ruwaito.
A wani labarin kuma Tsautsayi Ya Ratsa Yayin da Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa Ya fadi Ya Mutu a Kano
Dakarun 'yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekara 18 a duniya, Saminu Bala, bisa zargin kashe abokinsa a jihar Kano.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace saɓani ne ya shiga tsakaninsu, Bala Ya daki Khalil.
Asali: Legit.ng