Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Gwamnonin Arewa Biyu a Fadarsa Abuja

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Gwamnonin Arewa Biyu a Fadarsa Abuja

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin wasu jihohin arewa biyu a fadar Aso Villa yau Alhamis
  • Gwamnonin da suka ziyarci Buhari sun haɗa da gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, da na Kebbi, Atiku Bagudu
  • Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC ke ci gaba da shirye-shiryen fara yakin neman zaɓen shugaban kasa na 2023

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC biyu daga arewacin Najeriya.

Gwamnonin da suka ziyarci shugaban kasa a fadarsa Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja sune, gwamnan Jigawa, Atiku Bagudu da gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu.

Shugaba Buhari, Badaru da Bagudu.
Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Gwamnonin Arewa Biyu a Fadarsa Abuja Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin kafafen watsa labaran zamani, Buhari Sallau, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2023: Daruruwan 'Ya'Yan APC a Mazabar Gwamnan Arewa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

"Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karbi baƙuncin gwamnonin jihohin Jigawa da Kebbi a gidan gwamnati ranar 13 ga watan Oktoba, 2022," inji Buhari Sallau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotunan ziyarar gwamnonin biyu

Shugaba Buhari tare da Atiku Bagudu da Badaru.
Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Gwamnonin Arewa Biyu a Fadarsa Abuja Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaba Buhari Tare da gwamnan Jigawa.
Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Gwamnonin Arewa Biyu a Fadarsa Abuja Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya gana da gwamnonin cigaba, mambobin kwamitin gudanarwa da masu ruwa da tsaki.

Bayanai sun nuna cewa da yawan gwamnonin sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka watsar da su a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa.

A wani labarin kuma kun ji cewa Buhari ya Rantsar da Jastis Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Ariwoola Olukayode matsayin alkalin alkalan Najeriya.

Kamar yadda Buhari Sallau ya bayyana, an bashi rantsuwar ne a fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari a takaitaccen biki a Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku Na Shirin Kamfe a Kaduna, Wike Ya Ja Tawaga Zai Gana da Wasu Kusoshin PDP a Landan Kan 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel