Jerin Jami'o'in Najeriya 22 Da Suka Zabi A Dakatar Da Yajin Aikin ASUU
Biyo bayan umurnin da shugabannin kungiyar malaman jami'o'i na kasa, ASUU, sassa da dama na malaman jami'an yanzu sun zabi a dakatar da yajin aikin da suka shafe watanni ana yi.
Deborah Tolu-Kolawale, yar jarida mai aiki da The Punch, ce ta bayyana hakan a rubutun da ta yi a Twitter.
A cewar yar jaridar na makarantun gaba da sakandare, ga jerin jami'o'in da suka zabi a janye yajin aikin bisa sharadi ko umurnin kotu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yajin aikin ASUU: Jami'an da suka zabi a dakatar da yajin aikin
- Ladoke Akintola University of Technology (LAUTECH)
- The Federal University of Technology Akure (FUTA)
- University of Benin (UNIBEN)
- University Of Nigeria Nsukka (UNN)
- Tai Solarin University of Education (TASUED)
- Nnamdi Azikiwe University (UNIZIK)
- University of Lagos (UNILAG)
- Ekiti State University (EKSU)
- University Of Calabar (UNICAL)
- University of Port Harcourt (UNIPORT)
- Federal University of Technology, Owerri (FUTO)
- Adekunle Ajasin University
- Olabisi Onabanjo University (OOU)
- Kano University of Science & Technology
- University of Maiduguri (UNIMAID)
- University Of Jos (UNIJOS)
- Federal University of Agriculture, Abeokuta (FUNAAB)
- Alex Ekwueme Federal University
- Federal University of Technology Minna
- Kebbi State University of Science and Technology Aliero
- Usmanu Dan Fodio University Sokoto (UDUS)
- Bayero University Kano (BUK)
OAU ta gaza cimma matsaya
A bangare guda, an gano cewa ASUU na reshen Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife ta gaza cimma matsaya kuma yanzu tana jiran mataki da majalisar zartawa, NEC.
NEC din za ta gana a yau ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba, don yanke shawara kan kuri'un da sassanta suka yanke.
An tattaro cewa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi, Aliero da Jami'ar Usman Dan Fodio ta Sokoto ta yarda a janye yajin aikin saboda umurnin kotu.
BUK ta zabi a dakatar da yajin aikin bisa sharadi.
Tolu-Kolawole ta ce dukkan sassan ASUU, illa na jami'ar OAU, sun zabi a dakatar da yajin aikin kan sharadi ko kuma umurnin kotu.
Gwamnati Za Ta Baiwa Malaman ASUU N50bn Kudin Alawus, N170bn Kudin Karin Albashi
Punch ta ruwaito cewa za'a mayar da ragamar biyan kudin alawus na ma'aikatan jami'o'in Najeriya hannun majalisar jagorancin jami'o'in gwamnatin tarayya daga 2024.
Hakazalika gwamnati za ta saki kudi naira bilyan hamsin (N50bn) don biyan kudin bashi na alawus da Malaman ke bi kafin lokacin.
Wata majiya cikin majalisar zartaswar ASUU ta bayyana hakan ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.
Asali: Legit.ng