An biya duka ‘yan kwangilan dake aikin akan hanyoyin gwamnatin tarayya kudaden su – Fashola
- Fashola ya ce babu dan kwangilan dake bin gwamnatin tarayya bashi
- Fashola ya ce gwamnatin bata son jinkirin wajen kammala ayyukan da taba 'yan kwangila saboda ta yi wa 'yan Najeriya alkawarin tituna masu kyau a lokacin damina
Gwamnatin tarayya ta ce ta biya duka ‘yan kwangilan dake aiki akan hanyoyin gwamnatin tarayya a fadin kasar basussukan su.
A sanawar da ministan Wuta, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya fitar, ya ce babu dan kwangilan da ke bin gwamnatin tarayya bashi, saboda haka gwamnati bata son jinkiri wajen gyara da gina sabbin hanyoyin da taba da kwangilan su.
Shekaru biyu da suka gabata, ‘yan kwangilan dake aiki akan manyan hanyoyin gwamnatin tarayya suka yi korafin cewa ba a biya su basusukan biliyoyin kudi da suke bin gwamnatin tarayya ba, wanda yasa dukan su suka yi watsi da kwangilolin da aka basu.
KU KARANTA : Son kai ya sa Obasanjo ya kafa kungiyar siyasa – Matasan Arewa
Fashola wanda yayi jawabi ta mai magana da yawun bakin sa, Hakeem Bello, yace babu dan kwangilan da yake bin gwamnati tarayya bashi saboda haka ba a son jinkiri wajen kammala ayyukan da gwamnati ta basu.
"Duk wani dan kwangila da ya saba umarnin mu, mun san yadda za mu dashi, saboda mun yiwa ‘yan Najeriya alkwarin hanyoyi masu kyau lokacin damina," inji Fashola.
Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito labarin Naira Tiriliyan 1.2tr da gwamnatin Buhari ta saka domin yin wasu manyan ayyuka a fadin kasar nan inji Fashola
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng