Shin Ko Kun San Babu Buƙatar Cire Dattin Kunne Kwata-kwata?

Shin Ko Kun San Babu Buƙatar Cire Dattin Kunne Kwata-kwata?

Wani likita yayi cikkaken bayani game da muhimmancin kula da wasu gaɓɓai na jikinmu, Inda ya bayyana babu buƙatar goge kunnuwanmu kwatakwata

Wani likita mai ƙwarewa a fannin kunne, da hanci da maƙoshi, mai suna Chijioke Anekpo, ya bayyana wasu abubuwa da ka iya yi wa kunne lahani.

A hirarsa da jaridar Premium Times ya amsa wasu tambayoyi game da lafiyar wadannan sassan jiki uku.

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mai Tambaya: Shin ko amfani da iyafis ko waya na haifar da wata matsala ga kunnuwanmu?

Chijioke: A, amma ya danganta da irin waƙa da kuma ƙarfinta da ke fitowa daga jikin iyafis ɗin.

Na biyu, in iyafis ɗin na da datti kuma ba a goge ba, to zai iya haifar da wata cuta ga kunnuwan. Don haka, ƙarfin muryar na iya lalata kunne.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saboda haka, yawan amfani da iyafis na tsawon lokaci ba shi da amfani, za a iya amfani da shi na lokaci zuwa lokaci.

Tambaya: Ya batun shigar kumfar sabulu ko masu sinadaran tsaftar jiki da ka iya shiga kunne a yayin wankan? Shin suna da wata illa ne?

Chijioke: Ba su da wata illa. Ruwa na shiga kunne ai a kodayaushe, har da irin waɗancan sinadaran, amma suna fitowa ai. Babu wata illa saboda ai ba sa daɗewa a ciki. Da zarar an goge shikenan.

Tambaya: Ya kuma batun goge kunne da tsinken goge kunne, shi akwai wani hadari ne?

Chijioke: Ba ka buƙatar goge kunnuwanka, su suna iya goge kansu da kansu. Sai dai da yawan mutane ba su san haka ba. Tun daga ranar da aka haife ka har mutuwa, babu wanda yake iya goge kunnensa. Muna kawai goge fatar kunnen ne.

Kara karanta wannan

Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane

Don haka, game da cikin dodan kunne, babu buƙatar goge shi, yin hakan ma ɓata lokaci ne.

Akwai ma hatsari a ƙoƙarin goge kunnen da kanka. Sosan goge kunnen na iya cirewa daga kunnen ya faɗa, sannan a ƙoƙarin cire shi muna iya yin lahani ga kunnuwan.

Don haka, tsinken goge kunne ba shi da wani amfani kuma sojan sa ɓata kuɗi ne kawai da ma ƙoƙarin yin wa kunnuwanka lahani.

Tambaya: Shin shan ruwan sanyi na da illa ga maƙoshinmu?

Chijioke: Shan ruwan sanyi ba shi da amfani. Idan kana da saurin kamuwa da sanyi, to zai maka illa ta hanyar sa ka tari da wasu cutukan, amma in ba ka yi, shikenan.

Tambaya: Ina ga batun ruwa mai ɗumi kuma?

Chijioke: Za ka iya shan ruwan ɗumi, amma ba mai zafi ba saboda zai iya koma maka maƙoshi.

Tambaya: Ya kuma batun aske gashin hanci, shin akwai wata matsala tattare da yin hakan?

Kara karanta wannan

An damke Soja yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga AK-47

Chijioke: Wannan gashin na cikin hanci yana ba shi kariya ne idan ka shiga wuri mai ƙura, yana taimakawa ne.

Yana tare dattin cikin ƙurar daga shiga kafar iska ta hancin. Don haka, aske su ba shi da amfani. Za ka iya rage shi idan yana damunka.

Tambaya: Ina ga batun sakace hanci?

Chijioke: Wannan yana iya kawo zuban jini. Don haka, a kauce wa hakan. Saboda idan kana sakace hanci, za ka iya ganin wani ɗan ja-ja, wannan yana iya kawo zuban jini.

Guje wa yin sakacen shi ya fi amfani.

Tambaya: Shin amfani da takunkumin fuska yana da wata illa?

Chijioke: Ya danganta da wace irin matsalar mutum ke da ita tuntuni. Ga wanda yake da cutar ɗaukewar numfashi(asthma), sam sawar kuskure ce a gare shi na tsawon lokaci.

Mutum yana iya rasa ransa. Tana iya rage yawan numfashin mutum ko haifar da wani abu daban.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani Ta Koka Kan Yadda Ake Cigaba da Yi Musu Kisan Gilla

Amma idan lafiyarka ƙalau ka saka takunkumin na tsawon lokaci, to babu komai. Kawai ya danganta da yanayin lafiyar mutum.

Tambaya: Shin hayaƙi daga ababen hawa da itace na da illa ga lafiyarmu ko kafofin numfashinmu?

Chijioke: E. Hakan na iya shafar zuciya ko hunhu, duk da cewa hakan ya ta'allaka da yawan hayaƙin da mutum ke shaƙa.

Ba kamar ka shaƙa irin sau ɗaya ɗin nan ba ne, sai dai irin kodayaushe, shi ne yake da hatsari sosai.

Hayaƙi daga ababen hawa ma na iya kashe mutum saboda yana ɗauke da wani sinadari wai shi Kabon-mono-okzadi kuma suna gurɓata jini da kafofin shaƙar iska.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida