Bayan Shekaru 4 da Rasuwar Mahaifiyarta, Budurwa Ta Bayyana Bidiyo Mai Taba Zuciya na Yadda Rayuwa Ta Kasance
- Wata matashiyar budurwa ta saki bidiyo mai taba zuciya na halin da ta shiga bayan rasuwar mahaifiyarta da shekaru hudu da irin canjin da rayuwa tayi mata
- Ta fara da bayyana cewa ta musulunta bayan watanni kadan da mutuwar mahaifiyarta kuma ta kammala karatu tare da cigaba da wani a jami’a
- Sai dai budurwar tace ‘yan uwan mahaifiyarta maza da mata babu wanda ya sake waiwayarta ko kuma ya kira ta ko sau daya a cikin shekaru hudun
Bidiyon da wata budurwa ta fitar bayan rasuwar mahaifiyarta da shekaru hudu tana bayyana yadda rayuwa ta kasance cike da gwagwarmaya da fadi-tashi ya taba zukata.
Kamar yadda bidiyon ya yadu kuma arewafashion style suka saka a shafinsu na Facebook, budurwar ta labarta yadda rayuwarta da ta ‘yan uwanta ta kasance bayan mutuwar mahaifiyarsu.
Ta fara da bayyana cewa ta Musulunta bayan watanni kadan da rasuwar mahaifiyarta kuma ta kammala karatu a Poly.
Bata tsaya nan ba, ta bada labarin cigaban da aka samu a wurin ‘dan autansu amma kuma har a lokacin taurin kan da yake da shi yana nan bai daina ba.
Ta sake bayyana irin natsuwar da tayi da yadda ta gyara rayuwarta ta hanyar yin shiga ta gari a yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Bayani tun bayan da ki ka bar ni shekaru hudu da suka gabata. Na Musulunta bayan watanni da rasuwarki.
“Har yanzu bana son kwalliya kamar yadda ki ka sani. Cike da nasara na kammala karatun Physics a foliteknik kuma na samu gurbin karatu a jami’ar da nake buri.
“Na daina saka wanduna tare da bayyana tsiraicina. Auta yanzu tsawonsa ya kai kafa 5’9 kuma ya zama bakanike tare da kwarewa. Yana samun kudinsa na kansa.
Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri
“Har yanzu yana nan da taurin kasa, karuwa yayi kuma da kyar ake mu’amala da shi.
“Na ci karo da soyayya, sai dai ina tsoron zata kasance yadda taki ta kare.
“Nayi kokarin zama mai talla ga mai kwalliya.
“Bayan Shekaru hudu da mutuwarki, ‘yan uwan ki maza da mata sun yi watsi da ni. Basu taba kira su ji yadda nake ba ko sau daya.”
- Budurwar ta bayyana.
Bayan Shekaru 21 da Aure, Matar Manomi ta Haifa ‘Yan 5 Bayan Yara 13 da Take dasu
A wani labari na daban, a jihar Katsina, wasu mutane sun fara kwatanta Hajara Shuaibu matsayin matar da tafi kowa haihuwa a Najeriya bayan ta haifa yara 5 a ranar Laraba, 5 ga watan Oktoban 2022.
Tun farko dai Hajara ta haifa tagwaye har sau biyu,tazo ta haifa yara 9 daban-daban kafin ta haifa yara 5 a lokaci daya a makon da ya gabata.
Bata taba tsammanin zata haifa fiye da jinjiri daya ba don haka rayuwarta yadda ta saba take yi.
Asali: Legit.ng