Jerin Sunaye: Rikakkun Kwamandojin ‘Yan Bindiga 5 da Suka fi Bello Turji Hatsari a Zamfara
- Duk da fice tare da shaharar Bello Turji a matsayinsa na gogarman 'dan bindiga, akwai wasu 'yan bindiga da suka fi shi hatsari a jihar Zamfara
- Daga cikin mashahuran 'yan bindigan akwai Ado Aleru, Dan Ngala, Shadari, Halilu Buzu da Dogo Gudale wadanda barnarsu ta zarce ta Turji
- An gano cewa, sune wadanda suka jagoranci kai farmkain Jangebe, Tegina da sauransu kuma sun addabi hatta jihohi maus kusanci da Zamfara
Zamfara - Bello Turji mashahurin ‘dan bindiga ne da ya addabi yankuna da yawa na jihar Zamfara. Sai dai duk da shahararsa, kiyasi a kan tsaro wanda Zagazola Makama ya bayyana ya lissafo wasu kwamandojin ‘yan bindiga biyar da suka fi Bello Turji hatsari da shu’umanci a jihar Zamfara.
Ga jerin sunayensu da bayanai:
1. Ado Aleru
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Aleru na zama ne a Munhaye dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara kuma shi ne da alhakin hare-hare masu yawa a kananan hukumomin Tsafe da Gusau.
Suna addabar jihohi masu makwabtaka kamar Katsina tare da manyan hanyoyin Gusau zuwa Funtua.
2. Dan Nagala
Sansanin Dan Nagala yana nan a yankin Bozaya Mai Rai dake sakin Gandu dake hade kananan hukumomin Maru- Anka da Talata Mafara.
Shi ke da alhakin kai manyan hare-hare a kauyukan Maru, Talata Mafara, Bungudu da Maradun kuma suka sace ‘yan makarantar Tegina da na Jangebe tare da ajiye su a sansanoninsu.
3. Shadari
Shadari yana zama a sakin Gandu a kusa da iyakar Maru da Anka. Shi ke da alhakin kai miyagun farmaki a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum, Bakura da Gummi tare da jihar Kebbi.
4. Halilu Buzu
Halilu Buzu da babban abokinsa Umaru Nagona an gano sun koma dajin Magiri kusa da iyakar Maru da Anka a farkon daminar bana.
Shi ke da alhakin kai farmaki a Anka, Talata Mafara, Bakura da jihar Sokoto.
5. Dogo Gudale
Gudale yana rayuwa a dajin Fasa Gora dake karamar hukumar Bukkuyum. Shi ke da alhakin kai hare-hare a Bukkuyum da Gummi tare da kauyuka masu makwabtaka da jihohi Sokoto da Kebbi.
Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira
A wani labari na daban, mayakan ta’addanci na ISWAP sun halaka mayaka takwas na kungiyar ta’addancin Boko Haram a wata arangama da suka yi a Borno.
ISWAP tsagi ne ba kungiyar ta’addancin Boko Haram kuma sun rabe ne sakamakon rikicin shugabanci.
Asali: Legit.ng