Fitaccen Dan Siyasar Jihar Anambra, Nwobu-Alor, Ya kwanta Dama
- Ɗaya cikin mambobin da suka ƙirkiri jam'iyyar APGA, Chief Sylvester Nwobu-Alor, ya kwanta dama kamar yadda muka samu labari
- Marigayin ya kasance uban gidan ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi kuma hadiminsa lokacin yana gwamna
- Haka nan Nwobu tsohon ɗan majalisa ne a jamhuriya ta biyu kuma tsohon darakta janar na kungiyar yaƙin neman zaɓen Obi
Anambra - Daya daga cikin dattawan da suka kafa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Chief Sylvester Nwobu-Alor, ya rigamu gidan gaskiya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mamacin ya kasance uban gida kuma abokin shawarar dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar Labour Party a babban zaben 2023, Peter Obi,
Bayanai sun nuna cewa lokacin da Mista Obi ke matsayin gwamnan jihar Anambra, Marigayi Nwobu-Alor, ya taimaka masa wajen gyara tashoshin mota da Kasuwannin jihar a matsayin hadimin gwamna a wannan bangaren.
2023: Jam'iyyar APC Ta Sanar da Ranar Kaddamar da Tawagar Kamfen Tinubu Ta Mata Karkashin Aisha Buhari
Rahoto ya nuna cewa a wancan lokacin rikici da dambarwa sun yi katutu a Tashoshin mota, wanda ake zargin kungiyar direbobi NARTO da kitsa wa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma Nwobu Alor ya sha yabo bisa fani da kwarewarsa ta siyasa wajen dawi da zaman lafiya da tsaftace tsarin sufurin jihar, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Marigayi Nwobu Alor, tsohon ɗan majalisa ne tun jamhuriya ta farko kuma tsohon Darakta Janarna tawagar yaƙin neman zaɓen Peter Obi.
Kwale-Kwale ya kife da mutane a Anambra
A wani labarin kuma Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Nemi Mutum 30 Aka Rasa Sakamakon Kifewar Kwale-Kwale a jihar Anambra
Mutanen garin Umunnankwo a karamar hukumar Ogbaru suna cikin alhini bisa rasuwar ƴaƴansu maza da mata a hatsarin jirgin ruwa.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ruwan ya taso ne daga gadan Onukwu zai nufi kasuwar Nkwo da Ogbakuba a karamar hukumar ta Ogbaru.
Asali: Legit.ng