Gwamnan Bauchi Ya Umarci Ciyamomi 20, Kansiloli da Wasu Kusoshin Gwamnati Su Sauka
- Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya umarci Ciyamomi 20 su sauka daga kujerunsu bayan wa'adinsu ya ƙare
- A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar, umarnin ya shafi mataimakan ciyamomi, Sakatarori da Kansiloli
- Gwamnan ya gode wa mutanen bisa gudummuwar da suka bayar kuma ya musu fata nagari a harkokin da suka sa a gaba
Bauchi - Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya umarci shugabannin kananan hukumomi 20, mataimkansu, Sakatarori da Kansiloli su sauka daga muƙamansu.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wannan umarnin na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Asabar a Bauchi.
A cewar Gidado, umarnin ya zo ne kasancewar wa'adin mulkin zababbun shugabannin zai ƙare ranar 10 ga watan Oktoba, 2022.
Yace waɗan da umarnin ya shafa an umarci su da su miƙa harkokin tafiyar da ofisoshinsu hannun jagororin ɓangaren shugabanci a kananan hukumominsu ranar Talata 11 ga watan Oktoba, 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Ciyamomin da sauran jami'an gwamnatin da lamarin ya shafa zasu sauka ne gabanin shirya sabon zaɓe ko naɗa Kantomomi.
Hadimin gwamnan ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin yin ɗa'a ga dokar sashi na 2 (i) da ke ƙunshe a kundin dokokin kananan hukumomi na jihar Bauchi 2013 wanda aka yi wa garambawul, Punch ta ruwaito.
Ƙauran Bauchi ya gode wa Ciyamomi masu barin gado
Bugu da ƙari, sanarwan tace mai girma gwamna ya gode wa Ciyamomi, mataimakansu, Kansiloli da Sakatarori masu barin gado bisa aikin da suka yi wa jihar.
"Mai girma gwamna ya gode wa Ciyamomi masu barin gado, mataimaka, Kansiloli da Sakatarori bisa gudummuwar da suka ba jihar kuma ya musu fatan Alheri a harkokin da suka sa a gaba," Inji Sanarwan.
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Benuwai ya yi kira ga shugaban PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga mukaminsa
Samuel Ortom, gwamnan jihar da Ayu ya fito a arewa ta tsakiya, yace Ayu ya faɗa wa duniya a baya cewa zai sauka idan aka tsayar da ɗan arewa.
Gwamna Ortom ya shawarci Ayu ya ba da haƙuri idan ba zai sauka ba amma ba ya dinga cewa zangon mulkinsa na shekara huɗu bane.
Asali: Legit.ng