Jerin Sunayen Manyan Jigogin Jam'iyyar APC 16 Sun Koma PDP A Jihar Sokoto

Jerin Sunayen Manyan Jigogin Jam'iyyar APC 16 Sun Koma PDP A Jihar Sokoto

Yayinda aka fara yakin neman zaben 2023, akalla manyan jigogin jam'iyyar All Progressive Congress APC guda 16 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Sokoto.

Bikin sauya shekan ya gudana ne ranar Juma'a, 7 ga watan Oktoba, rahoton Vanguard.

Dukkansu shugabannin gunduma ne a Lajinge da Makuwana dake karamar hukumar Sabon Birni

sokoto
Jerin Sunayen Manyan Jigogin Jam'iyyar APC 16 Sun Koma PDP A Jihar Sokoto
Asali: UGC

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Alhaji Bello Goronyo, yayin tarbansu ya bada tabbacin cewa zasu ji dadin jam'iyar.

Hakan ya bayyana a jawabin da Hassan Shabi Sayinnawal ya fitar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"A PDP, ba ma nuna banbanci, mu na jama'a ne saboda haka ina muku alkawarin cewa zamuyi aiki tare domin gyara rana goben jihar da ma kasa ga baki daya."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Rasuwa A Canada

"Mun ji dadin tarayya damu da kuka yi kuma ina kyautata zaton zamu yi nasara a wannan jihadi."

A madadin wadanda suka sauya sheka, Alhaji Garba Dan-Sanda ya bayyana cewa sun yanke shawaran sauya PDP ne saboda namijin kokarin da mulkin PDP tayi a jihar.

Ga jerin sunayen wadanda suka sauya sheka:

Aliyu Liman,

Adamu Salihu,

Alinbo Dan-Tudu,

Abdullahi Belbela,

Abdu Langebo,

Hussain Langebo

Umaru Dadi

Abubakar Isa,

Agada Lajinge,

Usman Kalla,

Isa Suleiman,

Yawale Isa,

Jadi Abdullahi

Aminu Makuwana,

Alhaji Garba Dan-Sanda

Asali: Legit.ng

Online view pixel