Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Rasuwa A Canada
- Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, People's Democratic Party, PDP, tana alhinin rashin babban jigon ta
- A wannan karon, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Vincent Ogbulafor ne ya rasu a Canada yana da shekaru 73
- Da ya ke tabbatar da mutuwar sa, wani daga cikin yan uwansa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce marigayin ya rasu sakamakon wani ciwo da ba a bayyana ba
Tsohon Shugaban Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na kasa Cif Vincent Ogbulafor ya riga mu gidan gaskiya.
Vanguard ta rahoto cewa Cif Ogbulafor ya rasu ne a ranar Alhamis 6 ga watan Satumban 2022 a kasar Canada yana da shekaru 73.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan za a iya tunawa, Marigayin shine Sakataren Jam'iyyar PDP na farko.
Shi ɗan asalin garin Olokoro ne daga karamar hukumar Umuahia ta Kudu a Jihar Abia.
Cif Ogbulafor, wanda aka haifa a ranar 24 ga watan Mayun 1949, shine sakataren PDP na kasa na farko, kafin daga baya ya zama shugaban jam'iyyar na kasa bayan sa-in-sa da Sam Egwu da Senata Anyim Pius Anyim.
Menene ya yi sanadin murabus dinsa?
Amma, an tilasta wa marigayin yin murabus daga mukaminsa bayan rashin jituwa ya shiga tsakaninsa da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP.
Daga bisani an zargi Cif Ogbulafor da almubazaranci da kudi lokacin da ya riƙe muƙamin minista.
An rahoto ya sha bugun kirji yana cewa jam'iyyar PDP za ta mulki Najeriya tsawon shekaru 40 amma hakan bai zama gaskiya ba domin jam'iyyar APC ta karbi mulki hannunsu a shekarar 2015.
Jigon Jam'iyyar PDP a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Rasu a Asibiti
A wani rahoton, shugaban hukumar tsaftace muhalli ta jihar Bayelsa, Mista Mr Tolu Amatu, ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Bayanai sun ce Amatu, ya yanke ciki ya faɗi ba zato da daren ranar Asabar a gidansa da ke kusa da Titin Baybrdge a yankin Kpansia, Yenagoa, babban birnin jihar.
Sai dai an ce an garzaya da shi Asbiti domin kulawa da lafiyarsa amma likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.
Asali: Legit.ng