Jami’an Kwastom Sun Kama Bindigu, Harsasai, Buhun Shinkafa 7000
- Rundunar kwastom ta ƙasa ta yi nasarar kama wasu haramtattun kayayyaki masu yawa
- Sannan ta tattabatar da cewa kamawa da hana shigo da rigunan gwanjo wata hanya ce ta kiyaye lafiyar al’umma
- Hukumar tace gwamnati na ƙoƙarin ganin ta farfaɗo tare da ƙarfafa wa masu samar da tufafi guiwa a Najeriya
Wata rundunar jami’an kwastom ta ƙasa na reshen FOU-A a jiya, ta yi nasarar kama manyan bindigu biyu haɗin gida da ƙunshin alburusai 35 daga hannun masu fasa ƙaurinsu bayan wata ba-ta-kashi a kusa da Idi-Roko ta jihar Ogun.
Rundunar wannan yanki ta kuma tabbatar da ta samu kuɗi har naira miliyan 107 da dubu ɗari takwas na biyan kuɗin shigo da kaya.
A yayin da yake bayyana hakan ga manema labarai a jihar Lagos, jagoran wannan runduna kwanturola Husseini Ejibunu, ya tabbatar da an kama wasu kaya da aka riga aka biya wa kuɗin shigowa da ya kai N604m, rahoton Vanguard.
Ejibunu ya kuma yi ƙarin bayani da cewa kayayyakin sun haɗa da: buhunhunan shinkafar waje guda 7,328 masu nauyin kilogiram 50, da lita 121,550 na man fetur da kwalaye 68 na ƙanƙararrun naman kaji da kiret ɗin ƙwai da aka yi amfani da su wajen ɓoye shinkafar.
Sauran kayayyakin kuwa sun haɗa har da hodar iblis masu nauyin kilogiram 150 da jakunkunan masu launin kayan soja guda 10 da kayan gwanjo da kuma motocin; duk a watan Satumbar da ta gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A yayin da yake bayyana nasarorin da rundunar ta samu, ya tabbatar da cewa kotu ta yanke hukunci kan wasu manyan laifuka na wasu mutane shida da aka kama da fasaƙaurin wasu kayayyaki da kuma wasu da wasu ƙararraki guda shida da aka shigar a kan hukumar.
“Kwance kayayyakin gwanjon da aka yi nasarar yi kuwa, shi ne mafi girma da aka yi a wannan shekara, don haka mun tsunduma binciken a kan waɗanda suka yi wannan oda,” a cewar shugaban rundunar.
A yayin da yake yin ƙarin haske, shugaban rundunar ya cigaba da cewa:
“Ku sani, fasaƙaurin kayan da aka riga aka yi amfani da su na iya kawo naƙasu ga tattalin arziƙi da kuma lafiya ga al’ummarmu. "
A cikin hikima irin ta gwamnatimu, ta yin hakan ne domin ƙarfafa wa kanfanonin samar da tufafi na gida guiwa domin ingata harkar samar da tufafi a Najeriya."
"Wannan na zuwa ne a lokacin da ƙasashen duniya ke yin takatsantsan game da ɓular cutar nan ta Monkeypox wacce ke iya yaɗuwa ta hanyar tufafi da aka riga aka sa a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).”
Asali: Legit.ng