Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC Kan Rikicin Kwamitin Kamfe
- Jam'iyyar APC na kokarin dinke barakar da ya biyo bayan fitar da sunayen kwamitin kamfenta
- An ruwaito Shugaban uwar jam'iyyar APC ya tuhumci Asiwaju Bola Tinubu da kokarin mayar da su saniyar ware
- Hukumar Zabe ta INEC ta amince jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe daga jiya Laraba
Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Adamu, yanzu haka ya shiga zama da gwamnonin jam'iyyar guda shida tare da wasu jigogin jam'iyyar.
Jigogin sun hadu ne don tattauna rikicin da ya biyo bayan sakin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan Bola Tinubu.
Wannan zama na gudana ne a Sakatariyar APC ta Kasa dake birnin tarayya Abuja.
ChannelsTV ta ruwaito cewa daga cikin wadanda ke hallare a zaman akwai tsohon gwamnan Edo, Adams Aliyu Oshiomole da mataimakiyar kwamitin kamfe ta biyu, Hadiza Bala Usman.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnonin dake hallare kuwa sun hada Rotimi Akeredolu (Ondo), Abdullahi Ganduje (Kano), Abubakar Badaru (Jigawa), Simon Lalong (Plateau), Sani Bello (Niger), da Abdullahi Sule (Nasarawa).
A riwayar TheNation, mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur na wakiltar mai gidansa.
Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara
Rikicin da ya biyo bayan sakin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC ya dau sabon salo.
Shugaban uwar jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya aike wasikar kar-ta-kwana wa dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, rahoton Vanguard.
A wasikar da Adamu ya aike cikin dare, ya tuhumci Tinubu da saba alkawarin da yayi da mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar game da mukaman kwamitin yakin neman zaben.
Daga baya, Kakakin APC ya kartaya rahoton cewa Adamu ya yiwa Tinubu wannan zargi.
Asali: Legit.ng